Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya halarci Sallar Juma’a ta farko bayan ya hau karagar mulki.
Sarki Ahmed Bamalli wanda aka nada a ranar Laraba 7 ga Oktoba 2020 na halartar Sallar ne a Masallacin Fadarsa da ke Zariya.
Dubban mabiya sun yi cincirindo domin dagin Sarkin lokacin sallar jama’ar.
A ranar Alhamis masu zabar Sarki da kuma gidajen Sarauta na Masarautar Zazzau suka yi mubaya’a ga sarkin.
Ahmed Bamalli shi ne Sarkin Zazzau na 19, wanda kuma ya gaji surukinsa, Sarki Shehu Idris, wanda ya yi mulki na tsawon shekara 45 kafin Allah Ya yi masa rasuwa.
Kafin zamansa Sarki, Ahmed Bamalli shi ne Magajin Garin Zazzau kuma ya fito ne daga gidan Mallawa, daya daga cikin gidaje hudu masu sarautar Zazzau.