✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Saudiyya ya tattauna da Buhari

Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz ya kira Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta waya inda suka tattauna. A wayar da suka yi, Sarki Salman da…

Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz ya kira Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ta waya inda suka tattauna.

A wayar da suka yi, Sarki Salman da Shugaba Buhari sun tattauna hanyoyin bunkasa kawancen kasashensu domin alkinta alfanon da suke samu a tskakaninsu.

Kamfanin dillancin Labaru na kasar Saudiyya (SPA) ya ce shugabannin biyu sun yi tattaunawar ce a ranar Alhamis.

Ana iya tunawa a watan Agusta Sarki Salman ya kira Buhari a kokarinsa na ganin an sake daidaita farashin danyen mai bayan bullar annobar coronavirus da karya farashi.

Baya ga sauran bangarori da suka yi tarayya, Najeriya daga Saudiyya na kan gaba wurin yawan albarkatun man fetur wadanda kuma ake ganin man nasu na da matukar inganci.

Kasashen biyu na da fada fada a ji a kungiyar kasashe masu fitar da danyen mai ta duniya OPEC.

Ana iya tunawa cewa bullar annobar coronavirus tun a farkon 2020 ta kassasa harkar kasuwancin danyen maihar ta kai ga masu harkar na yin mummunan faduwa.