Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jagoranci addu’a ta musamman domin murnar cikarsa shekara guda a kan karagar mulkin Masarutar Kano.
Addu’ar ta musamman ta gudana ne a Babban Masallacin Kano a safiyar Talata, 9 ga Fabrairu, 2021.
- Maharan Dikwa sun so su yi wa sojoji yankan rago
- Kungiyar OPC ta kone kauyen Fulani ta kashe mace mai ciki a Oyo
- ’Yan bindiga: Rundunar Soji ta gargadi Sheikh Gumi kan lafuzansa
Aminiya ta halarci addu’ar, ga kuma kadan daga cikin hotunan da ta yi muku tsaraba kafin karin labarin ya biyo baya.
Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne Sarkin Kano na 15 daga gidan sarautar Sullubawa kuma an haife shi ne a ranar 1 ga watan Yuli 1961.
Ya hau karagar mulkin Masarautar ne a ranar 9 ga watan Maris, 2020, bayan Gwamantin Jihar Kano ta sauke Sarki Muhammadu Sanusi II.
Kafin zamansa Sarkin Kano, shi ne Sarki na Farko a Masarautar Bichi, wanda bayan saukarsa, dan uwansa, Alhaji Sanusi Ado Bayero ya zaman Sarkin Bichi.
Mahaifinsa shi ne Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero, wanda Allah Ya yi wa rasuwa yana da shekara 83 a ranar 6 ga watan Yuni, 2014 bayan shekara 50 a kan gadon mulki. Ana ganin Sarki Ado Bayero ake kuma ganinsa a matsayin sarki fami kima a zamanin mulkinsa.
Mahaifiyarsa ta fito ne daga gidan Sarautar Ilori a Jihar Kwara, kuma ya rike wasu sarautu a lokuta daban-daban kafin zamansa Sarkin Kano.