✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Ife ya sake zama gwauro bayan shekare 3

Matar Sarkin Ife ta rabu da shi baya shekara shekara da aurensu

Matar Sarkin Ife, Sarauniya Silekunola Naomi Ogunwusi, ta sanar cewa ta rabu da basaraken, bayan shekara uku da aurensu.

Karo biyu ke nan da auren sarkin mai daraja ta daya yake mutuwa, tun daga shekarar 2015 da ya fara hawa kan karagar mulki.

A sanarwar da ta fitar ranar Alhamis, Sarauniya Silekunola Naomi Ogunwusi, ta ce ba ta sha’awar ci gaba da zama da sarkin ko a danganta ta da shi.

A cewar sanarwar, “A yau ina sanar da cewa na bude wani sabon babi da sabuwar alfijir a rayuwata.”

Kafin fitowar bayanin nata, a kwanakin baya an yi ta baza ji-ta-ji-ta a baya, cewa auren basaraken da matar tasa ya mutu.