✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Ibbi ya yaba wa Buhari kan aikin gadar Ibbi

Sarkin Ibbi da ke Jihar Taraba, Alhaji Salihu Abubakar Dan Bawuro ya mika godiyar al’ummar Ibbi ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda isowar injiniyoyin da…

Sarkin Ibbi da ke Jihar Taraba, Alhaji Salihu Abubakar Dan Bawuro ya mika godiyar al’ummar Ibbi ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda isowar injiniyoyin da za su gina gada a garin Ibbi, hedkwatar Karamar Hukumar Ibbi a Jihar Taraba.

Sarkin ya ce isowar injiniyoyin babban alama ce ta fara aikin gina babbar gadar mota a kan Kogin Binuwai da ke garin Ibbi.

Sarkin ya nuna godiyarsa ce kan shirin soma gudanar da aikin a lokacin da wakilin Aminiya ya zanta da shi.

Ya ce an kwashe fiye da shekara 40 al’ummar Ibbi da ke Kudancin Jihar Taraba suna neman a gina gadar mota aka Kogin Binuwai da ke garin Ibbi amma hakan bai samu ba sai a yanzu.

Alhaji Salihu Dan Bawuro ya bayyana cewa isowar injiniyoyi garin Ibbi don soma  aikin gadar ya biyo bayan alkawarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dauka lokacin ziyayar yakin neman zabe a jihar.

Ya ce hakan ya nuna cika alkawarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi.

Sarkin ya ce yin wannan gadar zai bunkasa ayyykan kasuwanci da jin dadin jama’ar da suke jihohin Taraba da Adamawa da Gombe da wasu sassa na jihohin Borno da Yobe.

Ya kara da cewa gina gada a garin Ibbi na daya daga cikin babban burin al’ummar Ibbi da na daukacin jama’ar Kudancin Taraba.

Alhaji Salihu Dan Bawuro ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Taraba Mista Darius Ishaku da Sarkin Wukari Dokta Shekarau Agyo saboda kokarin da suka yi na ganin an cimma nasarar ganin Gwamnatin Tarayya ta amince da aiwatar da aikin gadar.

A karshe Sarkin ya ce za su ba ma’aikatan kamfanin da zai aiwatar da aikin goyon baya da hadin kai don a samu nasarar aikin.