✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawan Ife ya nada hakimai 42

Fadar Sarkin Hausawan Ile Ife a Jihar Osun, ta nada mutane 42 a matsayin hakimai da za su fara aikin wayar da kan al’ummar Arewa…

Fadar Sarkin Hausawan Ile Ife a Jihar Osun, ta nada mutane 42 a matsayin hakimai da za su fara aikin wayar da kan al’ummar Arewa a kan muhimman al’amuran da suka shafi kyautata dangantaka tsakaninsu da jama’ar gari da girmama dokokin kasa, domin samar da zama lafiya da kwanciyar hankali da zai kai su ga kusantar mahukumta, domin cin moriyar tallafin karatu zuwa manyan makarantu da samun guraben ayyuka ga ’ya’ya da jikokinsu da ke zaune a wannan masarauta ta Ile Ife, tushen Yarbawa.
An gudanar da bikin nadin ne a fadar Sarkin Hausawan Ile Ife, Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali, wanda majalisarsa ta amince da nada musu rawani da alkyabba da mika musu shaidar kammala karatu, domin tabbatar musu da mukaman. Unguwar Sabo, mazaunin Hausawa ne a garin Ile Ife, inda ta cika makil da al’ummar Hausawa da suka fito daga sassa daban-daban na kasa, domin halartar wannan gagarumin biki, wanda shi ne irinsa na farko da masarautar ta taba yi a tarihin kafuwarta shekaru 100 da suka wucewa.
Sarkin Hausawan Ile ife ya nada hakimai 42 da za su taimaka masa gudanar da mulki a masarautarsa. Mafi yawancin hakiman da aka nada, haifaffun garin Ile Ife ne da majalisar Sarkin ta ce ta yi la’akari da cancanta ne wajen nada su.
“Kafin mu nada hakiman, sai da muka kafa kwamitin dattijai a karkashin shugabancin Magajin gari Alhaji Mamman Sawaba da suka yi bincike a kan cancantar su da irin gudunmawar da suka bayar a baya, domin ci gaban masarautar Hausawan Ife da Jihar Osun da kasa baki daya,” inji Sarkin Hausawa Alhaji Abubakar Mahmuda Madagali, wanda ya shafe shekaru 25 bisa karaga. “Haka kuma sababbin hakiman, matasa ne masu ilmin addini da na zamani da suka gudanar da daukacin rayuwarsu a cikin Ile Ife da suka goge ta fannin cudanya da jama’ar gari da ake damawa da su cikin siyasa da bayar da gudunmawarsu ga harkokin kasuwanci, domin bunkasa tattalin arzikin Jihar Osun da kasa baki daya,” inji shi.
Sarakunan Yarbawa biyu wato, Lawarikan na Apoje, Oba Ademola Ademuluyi da Waasin na Ilare, Oba Olusola Akinriropo su ne suka wakilci Mai martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi a wajen bikin.
Shi kuwa Alhaji Bala Aliyu ’Yandoto shi ne ya wakilci ’Yandoton Tsafe, Alhaji Habibu Aliyu a yayin da Sardaunan Yamma, Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin, ya aika da tawagarsa a karkashin Sarkin Kudun Yamma, Alhaji Hassan Isiyaka Omo Oba. Shi kuwa Sarkin Hausawan Ore, Alhaji Abdullahi Bagobiri, shi ne ya jagoranci sarakunan Hausawa daga jihohin Yamma da jama’arsu da suka halarci biki
Daga cikin sababbin hakiman akwai Yarbawa biyu, masu suna Eluwole Akeem (Escort) da aka nada a matsayin Jagaba da Babatunde Oni (Trophy) da aka ba shi Magayaki da mace guda daya Hajiya Hadiza Aliyu dan Musa da ta samu sarautar Jakadiya. Sauran sun hada da Alhaji Abdul Azeez Muhammed da aka nada a matsayin Sardaunan Ife da Alhaji Muhammadu Shu’aibu Ore, Dallatun Ife da Alhaji Sani Abbas GNPP, Sarkin Yakin Ife da Alhaji dahiru Abubakar da ya samu mukamin Zannan Ife.
Makadan gargajiya da mawaka da maroka da masu busar Algaita da kakaki da ’yan farauta sun shere jama’a a al’adance a wajen wannan biki.