✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Sanusi II ya ziyarci Kano shekara 3 bayan tube rawaninsa

Ya samu kyakkyawar tarba daga masoya.

A karon farko tun bayan tube shi daga sarauta shekaru uku da suka gabata, tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ziyarci birnin Dabo a ranar Laraba.

Aminiya ta ruwaito cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano ne a karon farko tun bayan tube rawaninsa.

Gwamnatin Jihar ce dai ta cire shi a ranar 9 ga watan Maris din 2020, saboda abin da ta kira da rashin girmamawa ga ofishin Gwamna Abdullahi Ganduje.

Bayanai sun ce ya yada zango ne a birnin Kano domin ya gaishe da mahaifiyarsa, yayin da yake hanyarsa ta zuwa Dutse, babban birnin Jihar Jigawa, don yin ta’aziyyar rasuwar Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, sannan ya taya sabon Sarkin na Dutse murna.

Khalifan na Taijjaniyya a Najeriya ya samu kyakkyawar tarba daga masoya masu tarin yawa a filin jirgin sama na Kano, da kuma wadanda suka yi dakon zuwansa a gidan mahaifiyar tasa.

Lokacin da aka tube shi daga sarautar dai, an mayar da Sanusi garin Loko, daga bisani aka mayar da shi Awe, duka a Jihar Nasarawa.

Sai dai daga bisani, wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana ajiye shi a garuruwan a matsayin haramtacce, inda ta ce yana da ’yancin zuwa duk inda yake so.