A ranar Litinin din wannan makon 08-06-15, ce mai martaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya cika shekara guda daidai da zama Sarkin Kano na 14, a Daular mulkin Fulani, bayan rasuwar Baffansa Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, Sarkin Kano na 13, a ranar 06-06-15, bayan ya shafe shekaru 51 yana kan karagar mulkin gidan Dabo, wato tun daga Oktoba 1963 zuwa waccan rana. Ya bar matan aure da `ya`ya 64. A zaman kewayowar ranar an yi addu`o`i ga tsohon Sarki wajen nema masa rahama da kuma nema wa sabon Sarki jagora daga Allah. A cikin bukukuwan an gabatar da wata kasida mai taken gudumawar Sarki Ado a kan daukaka addinin Musulunci a zamaninsa, laccar da Gidauniayar Ado Bayero da hadin gwiwar Jami`ar Bayero da ke Kano suka shirya.
An kuma yi kwarya-kwaryan hawan daba da kewaye gari a kan dawakai inda Sarki Sanusi ya kai gaisuwa ga mahaifiyarsa mai babban daki Hajiya Saudatu da kuma gaisauwa da talakawansa, sannan kuma aka karkare bikin baki daya da sukuwar dawaki. Jama`a na kusa da na nesa sun samu halartar wadacan addu`o`i da bukukuwa.
Mai karatu bari mu dawo kan mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, wanda a bana yake dan shekaru 54, da haihuwa, dan Ciroma Aminu, jikan Sarki Muhammadu Sanusi Sarkin Kano na 10, wanda ba zuga ba ka ce tamfar tunda aka haife shi ya fara shirin ya shiga gidan magabatansa wato gidan Dabo. Idan ka yi la`akari da irin yadda ya samu ilimin addinin Islama da na zamani. Sarki Sanusi II, bayan ya samu digirinsa na daya da na biyu a kan fannin tattalin arzikin kasa daga Jami`ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarun 1981 da 1983, sannan kuma ya kama aikin Malanta a dai Jami`ar ta Ahmadu Bello a shekarar 1983 zuwa 1985. Ya kuma je kasar Sudan inda ya yi karatun digirin farko a kan fannin shari`a da addinin Musulunci.
Aikin Banki da ya shahara a kai ya fara shi ne da Bankin Icon Merchant Bank a shekarar 1985 har zuwa 1997. Daga nan ya matsa zuwa bankin UBA, inda ya zauna har zuwa 2005. Ya bar bankin na UBA a shekarar 2005 da matsayin Janar Manaja, ya koma First Bank a matsayin Babban Daraktan mai kula da sashen ba da rance da taurin bashi, fannin da aka yi ittifakin nan Sarki Muhammadu Sanusi II, ya fi kwarewa. Kafin likkafarsa ta daga ya zama Gwamnan Babban Bankin kasa a cikin watan Yunin 2010, sai da ya zama Manajin Daraktan Rukunnan Bankin First Bank din, kuma shi ne dan Arewa na farko da ya taba rike wannan mukami a tsawon tarihin Bankin na sama da shekara 100, da kafuwa.
Shigar sa Babban Banki ke da wuya, ya iya gano cewa kusan Bankunan kasuwancin kasar 15, daga cikin 25, da ake da su sun fara suma, musamman biyar daga cikinsu suna bukatar agajin gaggawa, bisa ga irin yadda Hukumomin gudanarwarsu da na Zartaswa, sun yi sama da fadi da dubun dubatar biliyoyin kudadensu walau ta hanyar ba kawunansu rance ko yin sama da fadi iri-iri. Bayan ya tallafa masu ya kuma sanya an gurfanan da irin wadancan manyan barayin zaune, don karbo kudaden jama`a da suka wawure, wasu ma har da dauri. Wannan aiki na gyaran Bankuna ya batawa mutanen shiyyar Kudu maso Yamma da na shiyyar Kudu maso Kudu rai matuka saboda su ya fi shafa, don haka suka mike haikan suna yakar Gwamnan Babban Banki, musamman ta kafofin yada labarai. Amma da rana daya Alhaji Sanusi Lamido Sanusi bai taba saurarawa ba, wanda da ya saurari soke-sokensu ya daina tsare-tsaren sanya Bankunan akan tafarkin da ya dace da a yau labarin da za a fabi akan tabarbarewar tattalin arzikin kasar nan da ya kasance mugun labari ga kusan duk `yan kasa.
A cikin irin waccan gwagwarmayar tabbatar da an yi kome cikin kamanta gaskiya da adalci, tsohon Gwamnan Babban Bankin a shekara 2013, ya bankado bacewar ko sace makudan kudaden man fetur har Dalar Amurka $20biliyan a hannun Kamfanin man fetur na kasa, wato NNPC. Wannan fallasa ta yi matukar ta da hankalin tsohon Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan, wanda ya nemi lalle sai Malam Sanusi Lamido ya janye, amma dai tsohon Gwamnan Babban Bankin, maimakon ma ya sassauta maganar, sai ya ci gaba da kuruwarta a inda ya samu damar yin magana. Hakan ta sanya ya rage watanni hudu, Gwamnan Babban Bankin ya kammala wa`adinsa na shekaru biyar, Shugaba Jonathan ya dakatar da shi.
Allah kuma cikin ikonsa kwana biyu da mutuwar mai martaba Sarki Ado, A ranar 08-06-15, Allah ya ba Alhaji Muhammadu Sanusi II, mukamin Sarkin Kano, nadin da ya haddasa zanga-zanga, bisa ga zargin wasu da suke da ra`ayin gwamnatin Kwankwaso ta yi masa Sarautar ne don ta kubutar da shi daga tuhumar zargin ya aikata ba daidai ba a lokacin da yake kan kujerar gwamnan babban Banki, wasu kuma suna zargin an yi zanga-zangar ne don wai ba daya daga cikin `ya`yan tsohon Sarki Ado aka nada ba.
Kome ke gaskiya ko rashin gaskiyar abin da ya sa akai waccan zanga-zanga, abin da ake magana dai a yau shi ne Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi II, yanzu ya cika shekara daya daidai a kan wannan Sarauta. Rahotanni sun tabbatar da cewa babban aikin da ya fara kuma har yanzu yake kai shi ne dinke barakar zumunci tsakaninsa da dukkan `yan uwansa musamman na cikin gidan Dabo, ta hanyar jawo wadanda za su jawu a jika da kwatanta masu gidan fa duk daya ne. Kuma shi mulki na Allah ne shi ke ba da shi ga wanda ya so a lokacin da ya so. Mai martaba San Kanon, ya kuma bullo da wasu manya-manyan ayyuka da za su kara inganta rayuwar talakawansa. A karkashin wannan shiri mai martaba Sarki yana kokarin hada dukkan garuruwa da kauyukan da ke cikin daukacin Masarautarsa da tsarin na`ura mai aiki da kwakwalwa, ta yadda zai iya magana ta na`urar komfutarsa, kai tsaye da Hakimai da Dagatai da masu Ungunni da mata Ungozoma ta wayoyinsu na hannu, duk da aniyar sanin me Masarauta da jama`a suke ciki, musamman a kan kiwon lafiyarsu da sauran matsaloli, don daukar mataki.
Ya kuma yunkura wajen gyara makarantar firamare ta cikin gidan Sarki, inda tuni ya kira Jami`an Bankuna, wadanda suka yi alkawarin za su sake tsarin makarantar ta hanyar mayar da ita ta gwaji, tare da wadata ta da kayayyakin koyo da koyarwa irin na zamani da kwararrun malamai. Ya gayyato wasu masana a kan ayyukan gine-gine da masu zuba jari a kan gina gidaje daga jihar Tetzas ta kasar Amurka da za su zo su fara gina gidaje 500, masu saukin kudi a filin Sarki da ke Unguwar Darmanawa ta karamar Hukumar Kumbotso kewayen birnin Kano, don sayarwa ga Talakawa. Sabon Sarki Muhammadu Sanusi tunda ya zo ya rungumi aikin ciyar da jama`a, walau ta ba su danyen abinci ko kuma dafaffe da ake kai wa asibitoci da gidajen marayu da na gajiyayyu a kullum.
Akwai kuma ayyukan ba da tallafi kudade ga marasa lafiya, walau a zaman kudaden sayen magunguna ko yin aiki ga marasa lafiya, baya ga masu zuwa fada a kulli yaumin, don neman taimakon kudade a kan bukatunsu na yau da kullum ko kuma wata alfarma. Na kusa da mai martaba Sarki sun tabbatar da dama can hannunsa da kofar gidansa bude suke don taimaka wa jama`a na kusa da na nesa.
Fatar wannan fili a nan bai wuce Allah ya kara kamawa mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi na II, ta yadda zai ci gaba da dorawa a kan ayyukan alherin da ya saba, Ya kuma kara masa imani da lafiya da jinkiri mai amfani, Ya raba shi da miyagun Fadawa. Ko yanzu an fara ganin kamun ludayinsa na alheri ne.