✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarautar Zazzau: Mutum 8 na hankoron darewa kan karaga

Gidajen Sarauta sun tsayar da masu neman zama Sarkin Zazzaun na 19 bayan rasuwar Shehu Idris

Mutum takwas daga gidajen sarautar Zazzau daban-daban na hankoron darewa kan karaga domin maye gurbin marigayi Sarki Shehu Idris.

Aminiya ta gano cewa zuwa karfe 5 na yammacin Alhamis wanda shi ne wa’adi na karshe da masu zabar sarkin suka saka, mutum takwas sun nuna sha’awar zama magadan Sarki Shehu Idris da Allah Ya yi wa rasuwa a ranar Lahadi.

Gabanin nan wani daga cikin ’yan sarautar ya yi korafin cewa bai san cewar a ranar za a rufe ba, kafin daga bisani ya mika takardarsa ta shiga takara.

Wata majiya ta ce, sharadin da masu zabar sarki suka saka shi ne a inda kowanne gidan sarauta ya gaza cimma matsayar fito da mutum daya, to gidan zai iya tsayar da mutanen da yawansu ba zai haura uku ba a matsayin ’yan takara.

Majiyar ta kara da cewa, “Saboda haka yanzu uku daga cikin gidajen sarautar Zazzau hudu ne suka tsayar da ‘yan takara suna bukatar samar da Sarkin Zazzau na 19.

  • ’Yan takara daga gidajen sarauta

“Gidan Katsinawa, inda daga nan ne tsohon sarki ya fito suna da ’yan takara hudu; Wamban Zazzau, Alhaji Abdulkareem Aminu, Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu; Dangaladiman Zazzau, Alhaji Aminu Idris da kuma Turakin Zazzau, Alhaji Aminu Shehu Idris”, inji majiyar.

Daga gidan Mallawa kuwa, Aminiya ta gano cewa mutum uku ne ke son zama sarkin wadanda suka hada da Ciroman Zazzau, Alhaji Sa’idu Mailafiya; Barden Kudun Zazzau, Alhaji Hassan Tijjani da kuma Magajin Garin Zazzau, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli.

Sai dai Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru ne kadai ya ke takara daga gidan sarautar Bare-bari, inji majiyar tamu.

A ranar Laraba Masarautar Zazzau ta rubuta wasika a hukumance zuwa ga Gwamnatin Jihar Kaduna tana sanar da ita labarin mutuwar tsohon sarkin.

Hakan na nufin da rubuta wannnan wasikar, an fara bin matakan nada sabon sarkin a hukumance.

Ana sa ran gwamnatin ta rubuta amsar wasikar wacce za ta kunshi matakai da ka’idojin da masu zaben sarki za su yi amfani da su kowanne lokaci daga yanzu.