Mutane sun yi ca a kan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano kan shirinta na gayyatar matashiyar nan ’yar asalin jihar da ta lashe Gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya, Shatu Garko da iyayenta zuwa ofishin hukumar.
A ranar Juma’a da dare ne dai Shatu mai shekara 18 ta lashe kambin gasar karo na 44 da aka gudanar a Legas, bayan matashiyar ta doke sauran ’yan takara 17.
- Yadda wasan mota ke jefa rayuwar matasa cikin hadari
- Real Madrid ta doke Athletic Bilbao babu ’yan wasa 11
Bayan labarin matashiyar mai sanya lullubi da ta lashe gasar ya karade gari, Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta sanar cewa ce za ta gayyace ta zuwa ofishinta tare da iyayenta kan rashin dacewar abun da ta aikata a matsayinta na Musulma Bakanuwa.
‘Haramun ne’
Shugaban Hukumar, Sheikh Haroun Ibn Sina ya shaida wa taron manema labarai cewa, “Bincikenmu ya gano Shatu Garko ’yar Jihar Kano ce daga Karamar Hukumar Garko kuma abin da ta yi haramun ne kada’an a Musulunci.
“Irin wannan rahsin kamun kai ba komai ba ne face kokarin ingiza mata su shiga wannan fitsara, alhali kuwa haramun ne ga mace Musulma ta bayyana jikinta, in banda tafin hannu da fuska, sai ga majinta ko muharramanta.
“Amma abin takaici sai ga shi yanzu ’ya’yanmu sun fara shiga wannan abu na rashin mutunci, abin kyama,” inji Sheikh Ibn Sina, wanda ya ce, nan gaba kadan hukumarsa za ta gayyaci iyayen matashiyar game da abin da ’yarsu ta aikata.
’Yancin Shatu Garko ne —CHRICED
Jin haka ke da wuya aka shiga caccakar hukumar gami da zargin ta da neman take wa matashiyar hakki, shisshigi, nuna bambanci da kuma rashin mayar da hankali kan abin da ya fi dacewa da aikinta.
Jami’ar Tuntuba ta Cibiyar Kare Hakki da Ci Gaban Ilimi (CHRICED), da ke Abuja, Zuwaira Umar, ta ce abin da Hisbah take son yi neman take hakkin matashiyar ce.
“Tana da ’yanci da kundin tsarin mulki ya ba ta na bayyana ra’ayi da mu’amala kamar sauran ’yan Najeriya; Sannan babu wata doka a Jihar Kano da ta haramta.
“Maganar rashin kamun kai kuma, ai abin da ta yi bai kai irin munanan shigar da ’ya’yan wasu manyan masu fada a ji a jihar suka yi ba.
“’Yar wani babban mai fada a ji Kano ta yi shigar da muninta ya fi ta Shatu Garko wadda shigarta a gasar ta fi ta sauran ’yan takarar mutunci.
“Abu na biyu kuma shi ne ba ma a Kano ta yi ba kuma ba a can take zaune ba,” inji Zuwaira.
Ta ce ba kyau kawai ake bi wajen zabar Sarauniyar Kyau ba, har da ilimi, fikira, taimakon al’umma da sauransu.
Hisbah ta fita batun Shatu Garko —Shehu Sani
Shi kuma tsohon dan Majalisar Dattawa, Sanata Shehu Sani, a tsokacinsa game da lamarin, cewa ya yi, “Shatu Garko ta shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya cikin shiga irin ta mutunci kuma ba ta saba tsari da al’adar ’yan Arewa ba.
“Amma akwai ’ya’yan masu kudi da masu fada a ji da suka yi hakan ba a ce musu uffan ba; Ina rokon hukumar Hisbah da ta kyale matashiyar.”
Hisbah za ta ga hauka —Aisha Yesufu
Mai rajin kare hakkin dan Adam, Aisha Yesufu, a nata tsokacin, cewa ta yi, “Don ’yata ta shiga gasar Sarauniyar Kyau kuma sai Hisbah ta ce ni za ta gayyata? Kai! Abin dariya!
“Ai ko da ranar za su ga tsabar hauka! Shiririta kawai! Ai ba wanda suka fi iya hayagaga da shirme!”
‘Hisbah na ja wa Musulmi abin kunya’
Marubucin Daily Trust, Gimba Kakanda, a tsokacinsa game da batun a shafinsa na Twitter ya ce, “Ina ganin Hisbah na jin dadin yadda ta mayar da Musulmai, musamman ’yan Arewa, abin dariya.
“Gayyatar iyayen Shatu Garko ba shi da amfani ko misakala zarratin, ko mene ne dalilin hukumar.
“Akwai muhimman abubuwan da suka fi wannan ci wa al’ummar Musulmi tuwo a kwarya.
“Sannan masu shiga gasar Sarauniyar Kyau ta Najeriya ba kananan yara ba ne.”