✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarauniyar ingila ta rasu tana da shekara 96

Bayan shafe shekara 70 tana mulki, Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta rasu ranar Alhamis. Tuni dai aka ambaci babban danta Sarki Charles a matsayin…

Bayan shafe shekara 70 tana mulki, Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta rasu ranar Alhamis.

Tuni dai aka ambaci babban danta Sarki Charles a matsayin wanda ya gaje ta.

Bayanai dai sun nuna kafin rasuwarta, sai da kafatanin ‘ya’yan nata suka hallara a gabanta, har zuwa lokacin rasuwarta.

Margayiyar ta yi jinya a gidan sarautar Balmoral karkashin kulawar likitoci, bayan da suka ce tana bukatar hutu.

Elizabeth ta fara milkin kadar tana da shekara 25, kuma a watan Nuwambar 1947 ne ta auri mijinta nargayi Philip Mountbatten, basarake daga kasar Girka da Denmark, inda suka shafe shekaru 73 tare, har mutuwarsa a watan Afrilun 2021.

Sun haifi ‘ya’ya hudu tare; Yarima Charles (Sarki a yanzu), da Gimbiya Anne da yarima Andrew da Yarima Edward.

Elizabeth ita ce sarauniya mafi dadewa a raye, da kuma akan karagar mulkin Birtaniya, sannan ita ce ta biyu a mafi dadewa a kan karagar mulki a tarihin duniya.