Bayan shafe shekara 70 tana mulki, Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ta rasu ranar Alhamis.
Tuni dai aka ambaci babban danta Sarki Charles a matsayin wanda ya gaje ta.
- Elizabeth: Sarauniya ta biyu mafi dadewa a kan mulki a tarihin duniya
- Za a kashe N1.2bn don gina manyan makarantu 18 a Arewa maso Gabas
Bayanai dai sun nuna kafin rasuwarta, sai da kafatanin ‘ya’yan nata suka hallara a gabanta, har zuwa lokacin rasuwarta.
Margayiyar ta yi jinya a gidan sarautar Balmoral karkashin kulawar likitoci, bayan da suka ce tana bukatar hutu.
Elizabeth ta fara milkin kadar tana da shekara 25, kuma a watan Nuwambar 1947 ne ta auri mijinta nargayi Philip Mountbatten, basarake daga kasar Girka da Denmark, inda suka shafe shekaru 73 tare, har mutuwarsa a watan Afrilun 2021.
Sun haifi ‘ya’ya hudu tare; Yarima Charles (Sarki a yanzu), da Gimbiya Anne da yarima Andrew da Yarima Edward.
Elizabeth ita ce sarauniya mafi dadewa a raye, da kuma akan karagar mulkin Birtaniya, sannan ita ce ta biyu a mafi dadewa a kan karagar mulki a tarihin duniya.