✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarakunan Hausawa ku rika kokarin tabbatar da haxin kan al’umma – Sarkin Yakin yamma

Sarkin Yakin Jihohin Yammacin Najeriya, Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan, ya nuna muhimmancin haxin kan al’umma, don haka ya nuna rashin jin daxinsa a kan rawar…

Sarkin Yakin Jihohin Yammacin Najeriya, Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan, ya nuna muhimmancin haxin kan al’umma, don haka ya nuna rashin jin daxinsa a kan rawar da wasu Sarakunan Hausawan Legas da ‘yan majalisarsu suka taka a kan batun naxa shi Sarkin Yakin Yamma da Allah (SWT) ya ba shi kuma Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin ya tabbatar masa.

Da yake yi wa Aminiya bayani a kan taron da waxannan Sarakunan Hausawa suka yi a fadar Sarkin Sasa a Ibadan inda suka nemi masarautar Sasa tawarware naxin da aka yi masa, Alhaji Isma’ila Maikankan ya ce, “Duk da yake basu samu biyan bukatar abun da suke so daga Sarkin Sasa ba amma a gaskiya bai kamata waxannan sarakuna su xauki irin wannan mataki ba. Ya kamata su canza salon mulkin ta yadda za a samu haxin kan jama’arsu da ci gaban su.

“Ku samr da hanyar kyautata zamantakewa tsakanin ‘yan Arewa da ke zaune a wannan sashe da sauran jama’a domin samar da zama lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya,” inji shi.

Ya ce, a ranar Lahadi 9 ga wannan wata (Yuli) ne dubbuanmutane na ciki da wajen Najeriya suka rufa masa baya zuwa fadar Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin da ke Ibadan domin halartar bikin tabbatar da naxa shi a matsayin Sarkin Yakin Jihohin Yamma.“A wannan rana Sarkin Sasa da kansa ya naxa mani rawani da sanya mani alkyabba tare da mika mani takardar shaida (certificate)da aka gudanar da wannan al’amari a gaban ximbin jama’a.” inji shi.

“Na samu labara kafin isowar wannan rana wai fadar Sarkin Hausawan Agege ta shigar da kara kotu tana neman a dakatar da naxa ni bisa wannan sarauta. Ni dai ban ga sammaci daga kotu ba, amma na sanar da lauyoyi na su yi bincike. A binciken ne suka gano cewa, waxanda suka shigar da karar sun yi barazanar aikawa da takardu ne kawai domin mu ji tsoro saboda ba a saurari karar ba. Haka kuma a ranar da muka isa fadar Sarkin Sasa sai muka tarar da waxannan mutane sun tura jami’an ‘yan sanda domin su dakatar da naxinna . A nan take Sarkin Sasa ya nuna musu takardar sammaci da aka aika masa daga Legas domin su gani ko akwai batun dakatar da naxina daga Alkali. Bayan sun karanta komai suka gane babu sanya hannun alkali a cikin takardar sai suka fice  daga cikin fadar suka yi tafiyarsu”

Alhaji Isma’ila Maikankan ya ci gaba da cewa, “Idan har sun san cewa, na yi musu wani laifi ne to don Allah ina rokon su su fito su gaya wa duniya irin laifin kowa ya sani. Muna zaman lafiya da dukkan jama’a da ke zaune a masarautar Hausawan Agege da Jihar Legas baki xaya saboda haka ban ga dalilin da ya sa suke so a warware wannan sarauta ba. Da farko ma na ki amincewa da karbar wannan sarauta ne, amma saboda shawarar jama’a da nake hulxa da su sai na amince.”

A game da neman gafarar Sarkin Hausawan Agege da aka ce ya yi sai Alhaji Isma’ila Maikankan ya ce, “wannan zance ba haka yake ba, domin na san girman iyaye da shugabanni kuma na yi wa iyaye na biyayya kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar kuma na rabu da su lafiya. Saboda haka irin wannan biyayya ce nake yi wa shugabanni a yanzu kamar yadda muka je fadar Sarkin Hausawan Agege, domin ya taya mu murna a matsayinsa na Uba kuma shugaban al’umma. Mun yi irin wannan ziyara zuwa fadar Sarakunan Lafiya da Keffi da suka taya mu murna, tare da yi mana addua, amma ban yi awa xaya a durkushe ina neman gafararsa ba saboda babu abin da na yi masa. Bai kamata mu rinka yin kalaman batanci haka kawai a tsakanin junanmu ba.”

Xan kasuwar tare da jama’arsa sun yi amfani da wannan dama wajen yin addu’o’in rokon Allah (SWT) Ya kara wa Shugaba Muhammadu Buhari lafiya ya dawo ya ci gaba da mulkin adalci ga jama’ar Najeriya. Sun yi fatan samun haxin kan jama’ar kasa da zama lafiya da kwanciyar hankali.”