Hakimin Gundumar Kwadom a Karamar Hukumar Yamaltu Deba, a Jihar Gombe Alhaji Muhammad Sani Abubakar, ya ce sarakunan gargajiya sun taka rawar gani wajen fadakar da jama’a muhimmancin zaman lafiya da yin sahihin zabe.
Alhaji Muhammad Sani Abubakar, ya ce kamar a garin Kwadom suna yin zama da talakawansa da masu ruwa-da-tsaki wajen ganawa a kan wayar da kan al’umma muhimmancin yin zabe cikin lumana da guje wa tashin hankali.
Ya ce, suna zama da jami’an tsaro da dattawan gari don tattauna matsalolin da ake ganin za su iya haifar da koma baya a lokacin zabe.
Hakimin ya ce su ma matasa wadanda su ne kashin bayan dimokuradiyya da kuma ci gaban al’umma wadanda da su ake amfani wajen tayar da hankali ana fadakar da su cewa, a zauna lafiya a tabbatar da an yi zabe mai tsabta ba tare da zubar da jini ko tashe-tashen hankula ba.
Hakimin na Kwadom, ya yaba wa dagatansa da jaurabai da shugabanin al’umma na yankin Kwadom bisa ga yadda suke ba shi hadin kai wajen ba da shawarwari kan zaman lafiya da kuma yadda suke taimakawa wajen ci gaban al’umma.
Ya gode wa Allah da Ya karbi addu’o’in da aka yi aka yi zaben Shugaban Kasa ba tare da samun rahoton tashin hankali ba.
Har ila yau ya gode wa Gwamnan Jihar Gombe da shugabanin addini Musulmi da Kiristoci kan yadda suke jajircewa wajen yin addu’o’i a masallatai da coci-coci tare da yin kira ga mabiyansu su zauna lafiya.
Alhaji Muhammad Sani Abubakar, ya ce jami’an tsaro ma sun taka rawar gani wajen hada kai da jama’ar gari suna ba su shawara kan muhimmancin zaman lafiya.
Daga nan sai ya ce suna samun lokaci musamman suna gudanar da addu’o`i ana yin yanka domin Jihar Gombe da Najeriya su zauna lafiya.
Ya bayyana cewa idan aka bai wa sarakuna dama za su bayar da gudunmawa fiye da yadda suke yi a yanzu. Kuma ya bukaci a daina dora kananan ’yan siyasa a kan sarakuna saboda a da sarakuna su ne alkalai su ne malamai kuma su ne ke zartar da hukunci, to yanzu ma idan aka sake ba su dama za su bayar da gudunmawa sosai.