✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Santin rake (1)

Wasu Kanawa ne su biyu, suna tafiya sai suka iske wani Bazazzagi a fadamarsa ta rake a Zariya, suka gaishe shi. Shi kuwa sai ya…

Wasu Kanawa ne su biyu, suna tafiya sai suka iske wani Bazazzagi a fadamarsa ta rake a Zariya, suka gaishe shi. Shi kuwa sai ya dauki sandar rake guda biyu ya ba su, sai suka zauna kusa da fadamar suna sha. Can sai dayan ya ce: “Da muna da kudi da mun sayi raken nan mun je gida mun yi ta sha.” Shi kuma dayan sai ya ce: “Kai amma da za a yi tashin duniya, da mu kam sai mu shiga fadamar raken nan mu yi ta sha.”
Daga Mudassir Ibrahim Mando Jihar Kaduna, 08024122559