✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sani Kiki: Bakaniken da ya ci jiya kuma yake cin yau

Alhaji Sani Ibrahim Kiki ya kwashe sama da shekara 50 yana sana’ar gyaran Babura. Shekarunsa 75 a duniya amma sai ga shi ya shiga cikin…

Alhaji Sani Ibrahim Kiki ya kwashe sama da shekara 50 yana sana’ar gyaran Babura. Shekarunsa 75 a duniya amma sai ga shi ya shiga cikin ’ya’ya da jikoki yana koyon yadda ake gyaran Keke Napep. Ta yaya ya faro wannan sana’a? Aminiya ta tattauna da shi kuma ga abin da yake cewa:

Sunana Alhaji Sani Ibrahim, wanda aka fi sani da Kiki Mai Gyaran Babur A Gindin Kuka, Bakin Kasuwa cikin birnin Zariya. An haife ni a Zariya. Na yi karatun Muhammadiyya a gaban iyayena, kafin in tafi Jos da zama. Daga nan sai Allah Ya hada ni da wani Ibo, Okah Chukwu Nwanyawu, wanda shi ne ya fara koya mini gyaran Babura.
A lokacin a saman dutse muke aikinmu komai ruwa kuma komai dari. Haka muka zauna da ogana har Allah Ya sa na fara iya gyaran babura sosai. Muna tare da shi ya ce zai koma gida. Ya ce ka ga wannan sana’ar da na koya maka, ka rike ta da kyau. In ka tsare gaskiya za ka ji dadinta nan gaba. Daga nan sai ya kawo guduma da sifana ya ba ni, ya ce to idan Allah Ya kara hada mu, za mu hadu. In kuma ba mu hadu ba shi ke nan. Ya kawo ’yan kudi kankani ya mika min. Sai hawaye ya fara zuba a idona, domin ya rike ni da gaskiya. To ashe akwai abun da zai faru a kasar ba mu sani ba. Bayan ya tafi garinsu ba da dadewa ba sai hadarin yakin basasa ya hadu. Daga nan ni ma sai na tattaro kayana, na nufo gida Zariya kuma har ila yau ban sake jin duriyarsa ba.
A Zariya sai na samu waje nan gindin kuka, na fara gyran babur. To ana cikin haka sai aka busa begilar daukar soja, sai na shawarci iyayena domin ni ma na shiga aikin soja. Suka ce min ba su yarda ba soboda suna shirin yi mani auren fari. Ni kuma na bi umurninsu, na hakura amma duka da haka mun koyi yadda ake kare kai ko da wani abu ya taso. To daga nan sai yaki ya barke. Bayan yakin ya lafa sai na ci gaba da sana’ata ta gyaran babur.
Ke nan kai ne mutum na farko da ya fara sana’ar gyaran babur a Zariya?
Na sami mutum uku suna sana’ar a wancen lokacin, Alhaji dan’inna a Wusasa sai kuma Alhaji Na’Allah a Babban Dodo, sai kuma wani dan Birom a Tudun Wada Zariya. Wadannan su na tarar a lokacin amma bayan na fara gyara, idan na yi wa mutum gyaran kafireto ko kuma wankin salansa sai ka ji ana cewa ai sabon inji ne na sa wa mutum; har a yi ta gardama. Sai a zo wurina sai na ce a’a, ai ba sabon injin ba ne, ku duba lambar babur dinku za ku ga ya yi daidai da shi. Haka na yi ta samun sa’a, mutane suna ta zuwa wurina domin in yi musu gyara. Kafin wani lokaci in dai gyran babur ne, to kusan sunana ya fara kaiwa ko’ina.
A wancan  zamanin, wadanne irin babura kuke gyarawa?
A lokaci akawi babur mai suna BSA da kuma mai suna Mobilite, sannan Suzuki da Yamaha da Roadmaster da Honda Beli da kuma Bespa da saurasu.
Ga shi ka shiga cikin yara domin kai ma ka shiga zamani, yaya ka ji, ga ka cikin ’ya’yanka da jikoki kana koyon abu daya da su?
Ai ka san masu iya magana sun ce gemu ba ya hana ilimi kuma girman kai rawanin tsiya. Don haka duk mai tunanin idan zamani ya zo to kai ma ka yi kokari ka shiga zamanin a tafi da kai, idan zamanin mai kyau ne. Don haka ka ga ni nan ina koyon yadda ake gyaran Keke Napep, don shi yanzu ake yayi kuma na ji dadi kwarai da gaske; domin kusan duk wadada muka hadu da su a nan suna girmama ni har da malaman da suke koya mana da wadanda muke koyan gyaran da su.
Ko za ka iya tuna yawan mutanen da ka koya wa wannan sana’a?
Abin da wahala, sai dai kawai mu yi mamure amma akalla sun kai kamar mutane dari kuma wadansu duk sun zama magidanta. Kuma ina gode masu, domin za ka ga wadansu sun zo sun duba ni har ma su kawo mini alheri. Don haka ina jin dadi kuma yanzu haka yaran da muke tare da su a nan tsakanin ’ya’ya da jikoki da kuma ’ya’yan makwabta, sun kai mutum 25 a yanzu.  
Wace irin matsala ka fuskanta a harkar nan da ba za ka mance da ita ba?
Ba a rasa matsaloli ba, tun da ni bawane na Allah. Koda matsalolin ma sun zo, ai sun wuce sai dai fatan alheri.
To abin dadi da faranta rai fa?
To wannan kam ai ba su lissafuwa, domin kuwa auren fari iyayena su suka yi mini amman sauran matana da na aura, ni na yi wa kaina ta hanyar wannan sana’ar kuma na je Makka na sauke farali kuma kullim ana samun biyan bukata. Na aurar da yara, babban abin farin cikina shi ne; kamar yadda ni ma aka koyar da ni, ni ma na koyar da wasu har ma sun zama mutane.
To wace shawara za ka ba ’yan baya, wato matasa?
Shawara ita ce, su zama masu hakuri da rikon amana da kuma biyayya da naciya a kan dukkan abin da suka sa a gaba, in dai na alheri ne.
Yawan iyalai fa?
Ina da mata hudu, ’ya’ya 20, jikoki 45 kuma ’ya’yana duk suna makaranta; wasu kuma na suna aiki kuma ina tare da wasu a nan. Don haka mun gode wa Allah kuma na gode muku.