✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanata Aduda ka kara karfafa dangantakar Musulmi da Kirista

Editan Aminiya jaridar al’umma, don Allah Ka ba ni dama in nuna gamsuwata kan yadda dan majalisar dattijai, Philip Tanimu Aduda ya hada kan Musulmi…

Editan Aminiya jaridar al’umma, don Allah Ka ba ni dama in nuna gamsuwata kan yadda dan majalisar dattijai, Philip Tanimu Aduda ya hada kan Musulmi da Kirista, a wajen buda bakin da ya shirya cikin azumin Ramadana. Hakikanin gaskiya wannan dan Majalisa da ke wakiltar Babban Birnin Tarayya ya cirri tuta, inda ya tara Malaman addini da Sarakunan gargajiya. Kuma a wajen wannan buda baki ya bayyana cewa haka ya taso ya gani a gidansu. Domin ba sa nuna wariya tsaknin Kirista da Musulmi.
Zai yi matukar alfanu idan dan Majalisa zai kara kaimi wajen fafutikar kyautata danganta tsakanin Kirista da Musulmi a makarantu da cibiyoyin ilimi da wuraren sana’o’in al’umma. Allah Ya karfafa gwiwar Aduda, ya kuma azurta mu da masu kwazo irin nasa, musamman a wannan lokaci da kasa ke fuskantar matsalar tsaro.  Daga Yakubu Takai 08133295651

Sakonnin waya

Gaisuwa ga Buba Galadima
zuwa ga dattijon arziki Buba Galadima ka yi hakuri wataran sai labari mu dai mun san kai ne kawai ka rage mana a yan siyasan akida a Arewa ba kada na biyu kudi mulki son a jika da sauran buri irin na ’yan siyasar Arewa bai dame ka ba. Allah Ya saka maka da alheri amin. Daga Nasir Musa.

Ga Buba Galadima
Aminiya,ina so ku ba ni daman a maida wa Buba Galadima Martani a kan amganar da ya yi na bnarin siyasa. Sako Daga Mu’azu S. Shehu
 
Ga dan majalisar Funtuwa
Zuwa ga Dokta Mansur Abdulkadir Al’ummar garin Mahuta da ke karamar Hukumar muna godiya ga mai girma dan majalisar Funtuwa/dandume bisa ayyukan alherin da yake mana, mun gode. Daga Usama Abdullahi Mahuta 08131347073.

Jaje ga mutanen Dutsen Jigawa
Ina tausaya wa al’ummar birnin Dutse, bisa rusa gidajen su da Hukumar Tsara Birnin ta DCDA ta yi. Gaskiya gwamnati ba ta kyauta ba, musamman a wannan watan mai alfarma ina ma a ce sai bayan sallah. Gaskiya an yi ba daidai ba. Kuma ina kira ga Shugaban hukumar, Alhaji Bashir Aminu ya gaggauta nema wa mutanen da aka tafka wa wannan rashin mutuncin matasugunni, domin lokacin damina ne. Daga AbdurRashid Ahmad Mustapha Birnin-Gwari, Abuja 08093535622.

Allah Ya ba mu mafita daga PDP
Salam Edita ka ba ni dama in yi tsokaci kan Wutar rikicin dake kara ruruwa a Jam’iyar PDP. Ko shakka babu rikicin da ya da baibayeta a lamu ne na rugujewar ta hadi da zama tarihi a shekara ta 2015. A lal misali a kwanan baya ta dakatar da Gwamnan sokoto, Aliyu Wamakko, ga Gwamnan Jihar Ribas Rotimi Amechi, duk wadanna a lamu ne na na rugujiwar ta. Duk a karkashin mulkin Jam’iyyar PDP babu zaman lafiya a Arewacin kasar nan! Ga Tashin bama-bamai Kashe-kashen kabilanci/ Addini/Siyasa Rashawa da Cin hanci. Ina addu’ar Allah ya kawo mana mafita daga mulkin jam’iyyar PDP. Ameen. Daga kasimu Aliyu Sardaunan Matasan Assada a jahar Sokoto. [email protected].

Gwamna Shema ka hukumomin tafi-da-gidanka
Assalamu alaikum. Edita, ka ba ni dama in bai wa Gwamna Shema na Jihar Katsina shawra kan lallai ya kafa hukumin tafi-da-gidanka, musmaman ganin yadda ya samu nasarar kula da lafiyar al’umma a birni da karkara, ta hanyar asibitin tafi-da-gidanka. Irin wannan dbara za ta yi kyau idan ka kafa dakunan karatu na tafi-da-gidanka, a bude cibiyoyin ilimi na tuntuba, ta yadda duk abin da ya shige wa mutumin Katsina duhu zai iya zuwa irin wadannan cibiyoyin don neman warwara. Allah Ya sa gwamnanmu ya dubi wannan shawrar da idon basira. Mun san za ka iya, tunda ka yi a harkar lafiya kow aya gani. Daga Hassan B. Nagado Jihar Katsina.

Ga Janar Babangida
Eduitasnm Amintattar jarida ina fatan za ka isar da sakona ga janar IBB. Naji cewatr a lokacin mulkinsa ya ba TY danjuma rijiyar mai. Matatu nawa ya kafa a kasashen ketare? To ga Arewa na cikin mawuyacin hjalin da kuka tsunduma mu. Daga Jamil Medicine 08039515906.

APC na damuna
Assalamu alaikum Aminiya APC suna ta damuna da za su kada PDP, ni kuma ban ga jama’ar da suke gubn da za su iya kada PDP ba, kuma ina son in tuna ma jama’ar APC da suke Arewa Yarbawa fa ba tabbas a wajen hadewa. Tun da aka fara siyasa PDP suke yi a kasashensu. Daga Saleh Zazzaga Jos Bukuru 08144406080.

Ga teloli
Assalamu alaikum Zuwa ga Edita, don Allah ina so ka ba ni fili in yi kira na musamman ga teloli, su dainma daukar alkawarin daba za su iya cikawa ba. Ku tuna fa Allagh zai tambayeku. Maasalam. Daga Uban dalibai Ranchass 08052659678.

Ga Jarumin fim A. Zango
Zuwa ga Adam A Zango. Don Allah Edita ka isar min sakona ga Adam Zango a kan yaji tsoron Allah ya daina yaudarar ‘yan mata. Don shi ma zai Haifa, kuma Allah zai iya saka wa a kan nashi yaran. Daga Ayshat Ibrahim 08093596418.

Me ya yi zafi Edita?
Edita kiri-kiri ka daina buga sakon Katsinawan Dikko. Ka tuna fa Aminiya bat a d amasoyan da sukla fi diyan Dikko masu albarka, karkashin Gwamna Dokta Ibrahim Shehu Shema mai albarka. Maigida Edita mene ne ya yi zafi haka shi ba wuta ba? Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.

Ga Najeriya
Allah Ya ba mu zaman lafiya a Najeriya amin. Daga PRO Tsalha Yaro Mabera 07068520028.

Ta’aziyyar Malam Lawal kaura
Aminiya don Allah ku isar min da sakon ta’ziyyata ga iyalan Malam Lawal kaura Zariya. Allah Ya jikan Malam, Ya gafarta masa, Yasa aljanna ce makomarsa. Allah Ya kyautata tamu in ta zo. Daga Mukhtar GZG496 Pharmacy MAkarfi L.G. 07063321997.

A kiyayi rawar gidan biki
Edita don Allah ka yi min izini in yi kira ga matan aure masu tikar rawa a gun bikin’ya’yansu, su ji tsoron Allah su daina. Edita Allah Ya fara tona asirin wata matar aure a gun wani biki tana rawa da girgiza ana yi mata liki sai zaninta ya kwance, gurin biki ya rude da ihu ana cewa sai “MAMA.” Abin haushi, abin takaici ita ce yayar ango. Daga Maryam Aliyu Garko A. Kano 08062568439.

Ga gwamna Yero
Edita don shugaban Annabawa ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna, Alhaji Mukhtar Ramadan Yero. Gwamna ka taimaki Jama’ar Dokan Karja a karamar Hukumar Kauru, saboda tun Makarfi na mulki ya ba da kudi domin a gina musu hanya, amma manyan Kauru sun cinye. Daga Barau Magaji 08148553725.

Masu juna ciki a hakura da hajjin bana
Ina kira gareku mata mahajjata bana, musamman masu dauke da juna biyu da su yi wa Allah da ananbi, su akre amrtabar su da ta Najeriyua. A yi hakuri da tafiya hajjin bana. 08055009634.

Ina Badiya ta shige?
Assalam Aminiya, don Allah ku tiamaka min da cigiyar wata baiwar Allah da muka hadu da ita a wannan shafin naku mai albarka, sunant aBadiya Sani Abdullahi, Unguwar kofar Gabas Bindawa, Jihar KAtsina. Daga Tasi’u Kurma kofar Mazugal Kano. 08097098548.

Ina gudunmuwar ilimi?
Assalamu alaikum. Aminiya ina yi muku fatan alheri. Don Allah ku yi kira ga shugabanni su yi nazarin gudunmuwar da suke bai wa ilimin Boko da na Addini. Shugabanni a duba. Daga ’Yar Gwal 08136894240.