Sana’ar dori na daya daga cikin sana’o’in gargajiya kuma take da muhimmanci a tsakanin sana’o’in gargajiya wadda a halin yanzu zamani na kokarin canja mata fasali daga yadda masu ita suka sani. A wasu sassan a iya cewa, sana’ar tana bisa hanyar bacewa baki daya. Wani matashin mai sana’ar wanda ya ce ya gaje ta daga kakanni ya yi wa Aminiya bayanin yadda sana’ar take da inda take haduwa da zamani:
Yaya tarihinka yake a kan wannan sana’a ta dori?
To sunana Lawal Jibrin, an haife ni a Unguwar Saulawa da ke cikin garin Katsina gidan Sarkin Dorin Katsina wanda marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nada da hannunsa. Ka ga ke nan na gaji yin dori.
To mene ne dori?
Abin da ake nufi da dori shi ne dashe ko saitawa ko hada wani abu wanda a da yake lafiya lau amma daga baya ya samu karaya ko gocewa ko tsagewa da makamantansu ga kashin mutum ko na wasu dabbobi. Ba dukan dabbobin ke karyewa ba a yi musu dori kamar doki. To da zarar mutum ya samu daya daga cikin abubuwan da na zayyana a sama, madorin gargajiya na gani ko ya taba zai gane abin da ya samu kashin. Kuma ana samun irin wannan matsala ce ta hanyar ko dai mutum ya fadi a kasa ba tare da ya shirya ba, ko hadari ko bugun wani abu da sauran irinsu. Wadansu kuma haka nan mutum zai karye ba tare da ya yi wani abu babba ba, wanda ke haddasa haka ba. Kuma ka sani cewa sana’ar dori in dai ta gado ce, to haihuwar mutunm ake yi da ita. Matar madori in ta samu ciki har ya kai wata 7 to za ta iya yin dori kuma ya yi lafiya lau, domin tana dauke da madori. Amma da zarar ta haihu kuma shi ke nan ba za ta iya ba saboda sun rabu.
Mene ne kayan aiwatar da ita wannan sana’a ta dori?
To duk mai yin dori za ka same shi da kara wanda yake goyawa bayan ya yi shimfida a lokacin da zai dora karaya. Amfanin wannan kara shi ne ya bayar da damar katangewa ko saita abin da ake dorawar don zama inda yake so ya zauna. Wato shi dai karan matallafi ne don gudun gocewar kashin da aka yi wa saiti aka dora. Shi ne ke hana bankarewar kafa ko hannun da aka dora bayan an warke. Har ila yau, sanya shi wannan kara ya kasu kashi biyu, wadansu suna sanya 5 zuwa 6,wadansu kuma yanke karan suke yadda zai iya zagayowa idan an sanya ga inda za a yi dorin. Amma mu dai a gidanmu ba mu wuce 6. Bayan kara sai tsumman da ake daurewa. Amma a yanzu muna amfani da bandeji ne na asibiti maimakon karan, karshe shi ne maganin da ake shafawa ga raunin.
Ko ka tuna dorin farko da ka fara yi?
To ba dori ne na fara yi na karaya ba, kamu ko in ce fitar da targade ne na fara yi kamar yadda al’adar gidanmu take idan za a koya maka. Kuma ina yaro ne shi ma wanda na yi wa yaro ne duk da ban iya tuna sunansa ba. To a wajen kamun targaden ne ake lura da yanayin mutum ta hanyar yadda za ka kama wajen rauni. Amma a matsayin dorin karaya, marigayi Malam Dan-Amina na fara yi wa dorin karaya, kuma a lokacin ina karatu a Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) ta Katsina.
Ta yaya kuke gane nau’in karaya?
To kasan shi sabo da abu yana sa ka san shi sosai kuma a kullum kana kara fahimtarsa, amma dai babban abin shi ne, lamarin Allah. Na sha fada wa mutane masu raunin cewa ga irin karayar da suke da ita, wadansu su yarda wadansu kuma in ce su je asibiti a dauki hoton wurin don su gani kuma har zuwa yau ba a samu akasin bayanin da nake yi ba. Ban mantawa, akwai wani mutum da na yi wa aiki na ce ya yi hakurin zama wuri daya na wani dan lokaci domin idan bai yi hankali ba, to kashin wajen gab yake da ya karye don dan abin da ke rike da shi ba wani abu mai karfi ba ne kuma har ya bari ya karye to zai dauki dogon lokaci bai warke ba. Sai bai amince da maganata ba, saboda yana ganin ba zai iya zama wuri daya ba. Karshe dai ya je asibiti don a yi masa hoto, ai daga nan bisa kujerar da ya zauna aka yi hoton bai yarda ya tashi tsaye ba balle ma ya taka kafar, saboda ya ga abin da na gaya masa haka yake.
An ce kuna da kishin junanku da zarar an ambaci sunan maidori to in ba shi ya yi dorin ba ba ya kyau. Yaya gaskiyar lamarin yake?
To ka san lamarin rayuwa yadda yake kowa da ra’ayinsa, kuma shi lamarin camfi yana gaba da komai a sana’ar gargajiya. Da yawa mutane sun dauka cewa da zarar an yi magana a kan abu to dole haka yake tabbata.
Sau tari kana magana ne a kan ilimin da kake da shi na abin da ka gani. An sha a kawo mini mutum nan, amma da na ga yanayin raunin sai in ce a je asibiti domin abin ba wajena ba ne, ba ma kamar in akwai zubar jini mai yawa.
Kuma batun a ce in an kai ka wajen wane ba zai iya ba sai wane, to karshe abin zai zamo shi wanda aka ambata shi ne a hakkun abin. Amma kurum da rana tsaka sai mutun ya shiga sana’ar don kawai ya ga ana samun wani abu bayan shi kuma bai gada ba. To duk irin aikin da zai yi da zarar an kai wa dan gado ya yi aikin to a irin haka ne waccan maganar ke shigowa.
Wace riba ka samu a sana’ar dori?
To, alhamdulillahi. Gaskiya babu abin da zance sai godiya ga Allah a kan abubuwan da na samu da wannan sana’a. Hatta da aikin da nake yi ta hanyar wannan sana’a na same shi. Duk wani abu da mutum ke bukata a rayuwa sana’ar dori ta yi mini shi. Wani abin da ba zan taba mantawa da shi ba a kan wannan sana’ar ce aka yi min kyautar gida da wani bawan Allah ya ba ni (an sakaya sunansa). Wannan mutum yana daya daga cikin masu fada a ji a Jihar Katsina. Allah Ya jarabce shi da samun karaya a kafa. Ni na yi masa dori, bayan na yi dorin, mutanensa da dama sun nemi a kai shi waje don a yi masa dori a asibiti don suna ganin kamar nawa bai yi ba ko kuma ba zai kai kamar na waje ba. Amma mutumin nan yace ba ya zuwa ko’ina, ya yi hakuri da wannan aiki da na yi masa domin yana jin dadi. A wancan lokacin har gwamnati ta nemi daukar nauyin kai shi kasar waje don yin jinya amma ya ki yarda. Ina zuwa sau biyu a kullum don duba shi. To a karshe dai da na ce masa zai iya fara takawa, sai kuma aka yiwo ca a kan cewa ana ganin kamar lokaci bai yi ba, amma dai ya bi umarnin da na ba shi. Allah cikin ikonSa Ya sanya ya mike tangaram. Sai kuma aka ce sai an je asibiti an dauki hoto don ganin yadda wurin yake. Duk wani bayanin da na yi na irin yanayin karayar da yadda aka yi ta, haka suka samu bayanin daga asibitin. To wannan aikin shi ya sa na zamo tamkar dan gida, domin ya ba da umarnin ko barci yake na zo a tayar da shi. In takaita maka wata rana kawai sai wani daga cikin mutanensa ya kira ni, bayan mun je wani gida, mun dudduba aikin da ake cikin yi masa, ban san cewa ni aka ba gidan ba sai bayan mun dawo. Sai kawai wanda muka je gidan tare ya miko mini mabudan gidan ya ce, “Alhaji ya ce a ba ka wannan gida kuma ka yi hakuri za a ci gaba da gyaransa.” Ai nan take na fara yin godiya kuma na ce, wallahi ni zan ci gaba da yin gyaran. Haka kuma ta faru a lokacin da na je can wajen Alhajin. Babu yadda bai yi ba a kan cewa in bari shi zai gama gyaran amma na ce, a’a, ni na yi. To wannan kyauta gaskiya na ji dadinta sosai. Kuma sanadiyar wannan sana’a na je jihohin Kudu da dama ina yiwo aiki. Gaskiya ba ni da abin da zan yi sai godiya ga Allah.
Yaya kake ganin sana’ar a yanzu ganin zamani na kokarin wucewa da ita?
To batun a ce zamani na kokarin wucewa da sana’ar dori sai dai a ce an zamantar da ita ba wai ya wuce da ita ba. Tunda ka ga muna amfani da bandeji maimakon tsumma, kuma muna cewa a je asibiti a yi hoto ka ga duk wani abu ne na zamanantar da sana’ar. Kuma in da gwamnati za ta yi kokari ta fitar mana da wani wuri da za mu yi asibitin masu dorin gargajiya da zai yi kyau. Sau da yawa mutanenmu suna fita waje amma ba su da masaniyar cewa mafi yawan asibitocin da ake kai su don a yi musu dorin ko gyaran kashin na gargajiya ne ba na Bature ba. To da za mu samu irin wannan dama da yawan cinkoson da ake samu a asibitocinmu da an samu sauki. Ba mu ki a hada mu da su likitoci na zamani ba, za mu yi aiki tare kuma a samu nasara. A yanzu haka, an sha a turo mana mutane daga asibiti mu yi musu aiki, wadansu kuma suke kawo kansu da kansu don rashin gamsuwa da na Baturen. Amma in aka yi mana wannan gata, ina tabbatar da cewa, asibitocin ƙashin da muke da su za a samu sauƙi. Kazalika zan yi amfani da wannan dama domin yin kira ga masu sana’o’in gargajiya ba sai na dori ba, mu yi kokari mu rika yin sana’ar tsakaninmu da Allah. In mai larura ya zo, in har ka san ba ka da abin da za ka yi masa, to kada ka rika yaudararsa kana amsar masa kudi, ba halal ka ci ba don za ka mayar a Ranar Karshe. Sannan kada mu rika rufe ido muna cewa sai an biya mu kudi kaza ko ba za mu yi aikin ba. Shi duk abin da ka yi sauki a kansa Allah zai saukaka maka.