Kasimu Abubakar (Ciyaman) Gidan Iddar Jihar Tawa a Jamhuriyyar Nijar, ya yi shekara 16 a Najeriya, yana sana’ar shayin ataye. Aminiya ta tattauna da shi inda ya ce sana’ar ta yi masa komai.
Mene ne tarihin fara wannan sana’a taka?
Sunana Kasimu Abubakar, ni mutumin Gidan Iddar ne a Jihar Tawa a Jamhuriyyar Nijar, na zo Najeriya ne domin koyon sana o’i. Kafin in fara sana’ar shayin Ataye, sai da na yi sana’ar nika kuma ban zo Najeriya ba da niyyar yin sana’ar Ataye ba. Amma da yake Allah Ya yi a wannan sana’a ta Ataye abincina yake, sai na rike ta a matsayin sana’a daya da nake gudanarwa yau kimanin shekara 16 ina yin ta a Najeriya. A lokacin da na zo Najeriya ba wannan sana’a ta Ataye ke raina ba, na zo ne domin in koyi Sana’o’i daban-daban domin idan na koyi sana’ar hannu zan koma kasata Nijar in rika koya wa matasan garinmu, amma Allah bai yarda ba.
Kafin in fara wannan sana’a ta Ataye sai da na fara sana’ar nika da injin a garin Mokwa na kuma zauna a Minna shekara 6 da Bida da Kwantagora da kuma Fatakwal, amma dukkan wadannan garuruwa da na zauna sana’ar Ataye na yi har zuwa yau da nake zaune a nan garin Birnin Kebbi yanzu haka ni ne Shugaban Masu Sana’ar Shayin Ataye na Jihar Kebbi.
Yaya wannan sana’a ta Shayin Ataye take?
Wannan sana’a ta sha bamban da ta masu sayar da shayin da ake zuba madara a hada da burodi. A da mutanen Najeriya ba su fahimci shan shayin Ataye ba, suna ganin Buzaye daga Nijar in sun zo wucewa da rakumansu, suna dafa shayin, to amma a wancan lokaci ba su fahimci magani ne ba. Sai su yi ta gani sun dauki shan sa tamkar ibada, amma ba su lura da irin yadda suke gudanar da harkarsu cikin kuzari ba.
To a hankali mutanen Najeriya suna shiga inda Buzayen suke, kuma ana ba su suna sha har suka fara gane amfaninsa, yanzu haka har suna son wuce mutanen Nijar yin wannan sana’a ta Ataye.
Hade-haden ganyen itatuwa ne, wadanda mafi yawansu daga waje ake shigo da su. Ana kawo su daga kasar China, kasar da ta shara a kan maganin gargajiya. Mukan samu wadannan ganyayyaki wadanda muke dafawa nan take mu bayar a sha. Akwai na maganin basir da zazzabi da rage kiba da sauransu.
Ko ka koya wa wadansu wannan sana’a?
Yanzu haka a nan cikin garin Birnin Kebbi ina da yara 7, kuma duk ’yan Najeriya, a kwanakin baya na yaye yara 15 yanzu daya daga cikinsu ana kiransa Haruna Sani har mota yake da ita a kan wannan sana’a ta Ataye.
Yaya kake ganin wannan sana’a?
A gaskiya sana’ar sayar da Shayin Ataye ta yi mini komai. Ka ga wannan ganyen shayin sai in dora a murhu sannan in dafa shi, idan na fito da safe kafin karfe biyu na rana na hada Naira dubu 5 ko 6. Bayan karfe 4 kuma in sake fitowa kafin Sallar Magriba na hada kusan Naira dubu 6 ko 7, domin da yamma an fi shan Ataye. Kuma maza da mata sha suke yi.
Me za ka ce kan zargin da ake yi cewa, masu wannan sana’ar na hada kayan maye a ciki?
Farkon shigowata Najeriya da na fara wannan matsala ta masu shan kayan maye, wadda kuma ita ce babbar matsalar da na fuskanta a wancan lokaci.
Amma sakamakon bijire wa wannan dabi’ar sai hakan ya kara janyo mini manyan mutane, kuma na gane akwai masu shigowa wannan sana’a da mummunar manufa, kuma na fadakar da ’yan kungiyarmu su tsabtace wannan sana’a, wanda hakan ya janyo har muka kafa kungiya. Ina tabbatar maka a yanzu idan har za a samu masu wannan dabi’a, to sai dai a boye.
Yanzu abin da ke ci mana tuwo a kwarya shi ne yadda jami’an Hukumar Shigi-da-Fici a Jihar Kebbi suke ci wa mutanenmu mutunci suna kama su ko ka nuna takardar izinin shigowa Najeriya ba su kyale ka sai sun kai ka ofis, sun bata maka lokaci. A halin gaskiya suna yawan damun mutanenmu ba gaira ba dalili, wannan yana tayar wa yaranmu hankali ba su da wani sukuni.
Ina kira ga hukumar da abin ya shafa ta rika tantance masu gaskiya da marasa gaskiya, kada a rika yi musu kudin goro.