✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samsung zai fuskanci karancin sabuwar wayarsa ta S6

Kamfanin Samsung ya fara sayarda wayarsa samfurin S6, amma kamfanin yana ta fafutukar ganin cewa wayoyin sun isa a kasuwa, amma hakan ya ci tura,…

Kamfanin Samsung ya fara sayarda wayarsa samfurin S6, amma kamfanin yana ta fafutukar ganin cewa wayoyin sun isa a kasuwa, amma hakan ya ci tura, kamar yadda kafar yada labarai ta BBC ta bayyana.

Kodayake Samsung ya yi hasashen riba a sabuwar wayar, amma ya damu game da lokacin da ake dauka na kera ta.
kwararru sun ce hakan zai iya sa masu sayen wayoyin dole sai sun yi oda sannan su jira.
Samsung na fuskantar gasa mai karfi daga Apple yayinda kuma wayoyi masu arha da ake samarwa a China suma ke yi kasancewa kalubale ga Samsung
Wani mai yin sharhi akan wayoyin salula Thomas Husson ya shaida wa BBC cewa kamfanin zai fuskanci matsala idan har wahalar da ke tattare da samar da sabuwar wayar shi ne yake janyo karancin ta.