✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samar da bashi mara ruwa ne zai bunkasa noma a Arewacin Najeriya – Farfesa Binta

An bayyana rashin samun bashi mara ruwa da manoma ke yi a fadin kasar nan a matsayin babban kalubale ga ci gaban harkar noma a…

An bayyana rashin samun bashi mara ruwa da manoma ke yi a fadin kasar nan a matsayin babban kalubale ga ci gaban harkar noma a bangaren Arewacin Najeriya, inda mabiya tafarkin addinin Musulunci suka fi rinjaye.

Daraktar Cibiyar Harkokin Bankin Musulunci ta kasa da ke Jami’ar Bayero (International Islamic Banking and Finance, Bayero Unibersity Kano, Farfesa Binta Tijjani Jibril ce ta bayyana haka a lokacin taron da cibiyar ta shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Jigawa.

Farfesa Binta ta bayyana cewa bangaren Arewacin kasar yana da duk abin da abin da ake bukata wajen tafiyarwa tare da ciyar da harkar noma gaba sai dai tunanin karbar bashi a bankuna kan zama babbar barazana ga manoman. “Arewa tana da komai na ci gaban noma sai dai kasancewar yawancin manomanmu Musulmi ne suna gudun karbar bashi mai ruwa daga bankuna, wanda hakan ke zama babbar barazana gare su wajen tafiyar da harkokinsu kamar yadda ya kamata, domin babu yadda za a gudanr da harkar noma ba tare da kudi isassu a hannun manomi ba. 

“Mun san yadda a baya yankin Arewa ya zama shi ke ciyar da kasar nan kaf abinci, baya ga shahara da yankin ya yi wajen noma don riba inda ake noma auduga da gyada, sai dai a yanzu wannan suna da suka yi yana neman gushewa ya zama tarihi, saboda rashin karfin jari a hannun manoman yankin”

Har ila yau Daraktar cibiyar ta yi kira ga gwamnati da ta samar da wani yanayi da za ta rika tallafawa harkar noma musamman a Arewacin kasar nan.

“Duk da cewa akwai shirye-shirye masu yawa na gwamnati don bunkasa harkar noma, sai dai har yanzu rashin samun bashi ga manoman na mayar da hannun agogo baya, domin kusan dukkanin tallafin da gwamantin ke bayarwa a harkar, bashi ne wanda ake dora kudin ruwa akai, hakan ya sa manoman dasuak fito daga Arewacin kasar nan ba su amfana daga gare shi. Don haka akwai matukar bukatar a samar da wata hanya da manoman wannan bangare na Najeriya za su amfana” Farfesa Binta Jibril ta bayyana bankin musulunci a matsayin hanya daya tilo da za ta dinke wawakeken gibin da ake da shi a harkar noma a kasar nan.

A nasa jawabin, Shugaban Jami’ar ta Bayero, Farfesa Muhammad Yahuza Bello wanda Mataimakinsa bangaren gudanarwa, Farfesa Idris Adamu Tanko ya wakilta, ya bayyana noma a matsayin babbar hanyar bunkasar tattalin arziki da kuma kakkabe yunwa a tsakanin al’umma.

Shugaban Jami’ar ya kara da cewa idan ya kasance manoma ba su da hanyar samun kudi don yin noma, to dukkanin wasu shirye-shiyen gwamnati don bunkasa harkar noma ba zai haifar da da mai ido ba.