Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce sama da ’yan Jiharsa 100,000 ne aka kashe a rikicin Boko Haram a cikin shekara 12 da suka gabata.
Ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake amsa tambayoyin ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja bayan ya gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya kuma ce sama da ’yan Boko Haram 2,600 sun mika wuya, ciki har da mata da kananan yara ya kuma ce ba dukkan iyalansu ba ne ’yan ta’adda.
Zulum ya ce wasu daga cikin yaransu sun sami horo kan sarrafa makamai, ciki har da bindiga kirar AK-47, inda ya ba da tabbacin cewa za a bi dukkan dokokin Najeriya da na kasa da kasa wajen magance matsalar.
Ya kuma yi bayanin cewa babu wata doka da ta ce a kashe dan ta’addan da ya tuba, inda ya ce daga cikinsu akwai wadanda ba su ji ba, ba su gani ba aka tilasta musu shiga kungiyar, yayin da wasu kuma yara ne kanana.
Gwamna Zulum ya kuma ce yana goyon bayan mika wuyan nasu ba tare da kowanne irin shakku a kansu ba.
Ya ce ’yan Boko Haram sun kai masa hari kusan sau 50, ya kuma yi alkawarin taimaka wa wadanda iftila’in ya shafa, musamman wadanda aka kashe wa iyaye.
Gwamnan ya kuma ce har yanzu ba a san inda kusan kaso 10 cikin 100 na mutanen Jihar suke ba, sakamakon aikin ta’addancin.
Ya ce ya tattauna batun mika wuyan ’yan Boko Haram din da Shugaba Buhari, inda ya ce shi ma bai ga dalilin da zai sa a ki karbar tasu ba.
“Shugaban ya yi maraba da rahoton mika wuyan. Kuma in dai ba so muke mu ci gaba da yakin da ba zai kare ba, ba mu da dalilin da zai sa mu ki karbar wadanda suke son mika wuya ba,” inji shi.