Salmanul Farisi yana Madina a matsayin bawan Bayahuden da ya saye shi, har Manzon Allah (SAW) ya yi hijira. Bai san da batun hijirar ba, saboda shagala da aikin bauta ga mai gidansa. Bari mu bi Salmanu mu ji daga bakinsa: Ya ce: “Lokacin da nake kan itaciyar dabinon mai gidana ina yi masa wasu ayyuka, shi kuma yana zaune a karkashinta. Sai wani dan Baffansa ya zo, ya tsaya a kansa ya ce: “Ya wane! Allah wadaran kabilar Ausu da Khazraj! Wallahi lallai ne su, sun hadu yanzu haka a kuba wurin wani mutum da ya zo daga Makka yana riya shi Annabi ne.”
Abin nema ya samu ga Salmanul Farisi, cikin rawar jiki da dokin neman karin bayani kan wannan labari Salmanu ya ce: “Ina jin maganarsa sai jikina ya kama karwa ina bare-bare mai tsanani har na ji tsoron kada in fado a kan mai gidana. Sai na sauka daga kan itaciyar dabinon nan na ce da Bayahuden da ya kawo wannan labari. “Me ka ce?” Sai mai gidana ya fusata, ya buge ni duka mai tsanani. Ya ce, “Mene ne gaminka da wannan batu? Ka koma zuwa ga abin da kake kansa na aikinka.”
Sai Salmanu ya koma kan aikinsa yana tunani a cikin zuciyarsa, “Shugabana ban zama bako ba, ban yi tafiye-tafiye har na zama bawa ba, face saboda kwadayin wannan haske da aka aiko Manzon Allah (SAW) da shi. Da ka san abin da nake ji ya shugabana da ka yi min uzuri, kuma da ka san cewa lallai ne ni, na zo wannan kasa ce domin haduwa da mafi alherin wanda ya taka kasa (SAW).”
Haka Salmanu ya rika tunani a cikin zuciyarsa yana aiki har ya kammala aikin da mai gidansa ya sanya shi.
Salmanu (RA) ya ci gaba da ba mu labarinsa ya ce: “Da yamma ta yi sai na dauki wani abu daga cikin dabinon na tafi zuwa ga Manzon Allah (SAW) a kuba, na ce: “Na ji labarin kai mutumin kirki ne, kuma kana tare da wasu sahabbanka da kuke baki. Wannan dabino da ke wurina na tanade shi ne domin sadaka, kuma na ga ku kuka cancanta da shi fiye da wasunku. Sai na mika masa, sai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku ci.” Ya kame hannunsa bai ci ba. Salmanu ya ce: “Sai na ce a cikin raina, wannan alama daya ke nan, ba ya cin sadaka. Sannan na tafi na tara wani abu daga dabino, na sake zuwa ga Manzon Allah (SAW), na ce masa: “Na ga ba ka cin sadaka, to, wannan kyauta ce na karrama ka da ita.” Salmanu ya ce, sai Manzon Allah (SAW) ya ci daga gare ta, kuma ya umarci sahabbansa suka ci tare da shi. Salmanu ya ce: Wannan na biyu ke nan, yana cin kyauta.”
Saura alama ta uku, Salmanu ya ce: “Wata rana na zo wucewa, daya daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW) ya rasu, sai Manzon Allah (SAW) ya fita jana’izarsa. Salmanu ya ce: Sai na je ga Manzon Allah (SAW) yana Baki’a, na iske shi zaune, na yi masa sallama, sannan na koma bayansa ina dubi zuwa ga gadon bayansa ko zan ga hatimin da Fadan Amuriyya ya siffanta min. Da Manzon Allah (SAW) ya ga na koma ta bayansa, sai ya fahimci ina kokarin binciken wani abu ne da aka siffanta min. Sai (SAW) ya dan ja rigarsa daga gadon bayansa, sai na ga hatimin, sai na gane shi ne. Sai na fada kan Manzon Allah (SAW) ina sumbatarsa ina kuka. Wace kasa ce za ta iya rike ni, wace sama’u ce za ta iya yi min inuwa! Domin hakika na ji a jikina cewa na riski sa’ada da rayuwa. A nan zaman lafiya da imani suke, a nan tafarkin zuwa ga Mai rahama da rabauta da Aljanna suke. A nan farin ciki da amana suke. Na shaida lallai babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Kuma na shaida lallai Annabi Muhammad Manzon Allah ne!”
Allahu Akbar! Salmanul Farisi ya karbi Musulunci ba tare da tunanin ubangidansa Bayahuden nan ba, ba domin komai ba, sai domin wannan ne abin da ya rabo shi da gidansu, ya rabo shi da garinsu. Wannan ne ya sa ya rabu da izza da daukaka da girman da ya taso cikinsu. Neman wannan shiriya ce ta sa ya yi ta ratsa garuruwa da kasashe har ya iske kansa a matsayin bawa! “Wanda Allah Ya yi nufin Ya shiryar da shi, sai Ya buda kirjinsa domin Musulunci.” (k:6:125). Tabbas wannan aya ta yi daidai da abin da Salmanul Farisi yake nema. Wannan aya ta dace da shi.
Rana da haske da shiriya sun haskaka, kuma duffan jahilci da bata sun ruguje, Salmanul Farisi (Allah Ya yarda da shi) ya karbi Musulunci. Yanzu kalubalen da ke gabansa, shi ne yadda za ta kaya a tsakaninsa da mai gidansa Bayahude. Shin zai amince Salmanu ya fanshi kansa domin ya ci gaba da yin sabon addininsa ko kuwa zai ki domin ya samu lasisin musguna masa?
To, amma da Bayahuden nan ya ga yadda Salmanu ya karbi sabon addinin nan nasa da irin karfin imaninsa, sai ya yanka masa kudi ko aikin da zai biya ko ya yi ya fanshi kansa, ya zama ’yantacce.
Sai Salmau ya fanshi kansa ya zama ’yantacce. Bayan Salmanu (RA) ya ’yanta kansa sai sahabbai suka shiga rububi a kansa, kowa yana son a jingina Salmanu da zuriyarsa. Abubakar Siddik (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Salmanu yana daga cikinmu Alu Tamim.” Sai Umar (Allah Ya yarda da shi) ya ce: “Salmanu yana daga cikinmu Alu Adiy.” Sai Annabi (SAW) ya daga muryarsa yana kira yana cewa: “Salmanu yana daga cikinmu Alu Baiti.”
Mutumin kirki ke neman jingina da mutumin kirki, kuma mutumin kirki ake neman jawo shi a jiki. Wannan ne abin da Salmanu ya iske kansa. daukakar da ya baro a Farisa domin neman shiriya ga ta ta dawo har ma ta fi wadda ya baro. Ga Amirul Muminina kuma halifa na farko yana neman Salmanu ya kasance daga zuriyarsa. Ga Amirul Muminina kuma halifa na biyu shi ma yana neman a jingina Salmanu ga zuriyarsa. Can kuma uban tafiya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa’alihi Wasallam) sai ya yanke hukunci cewa Salmanu yana daga Ahlul Baiti ne!
Tirkashi! Daga gidan bautar wuta zuwa gidan hasken Annabta! Wannan sai mai neman shiriya na gaskiya, wannan ba na mai neman karatu ko ilimi ne kawai ba, domin ilimi da karatu daban, shiriya daban. Duk da ba a samun shiriya sai da karatu ko ilimi, amma karatu da ilimi ba su ne shiriya ba, matakai ne na neman shiriya. Shi ya sa Salmanu ya rika neman mutanen kirki a cikin malaman addinin Nasara ya zauna a karkashinsu, wadanda a karshe suka shiryar da shi zuwa ga Manzon Allah (SAW).
Saboda karfin imanin Salmanul Farisi (RA) da shaukinsa na neman shiriya, ya sa Annabi (SAW) ya ba da shaida kan gaskiyar imaninsa. Buhari da Muslim sun ruwaito cewa” “Lallai Abu Huraira (RA) ya ce: “Mun kasance a zaune a wurin Annabi (SAW), sai aka saukar masa da Suratul Jumu’ati cewa: “Da wadansu mutane daga gare su, ba su i da riskuwa da su ba.” Sai na ce: “Suna daga su wane ne ya Manzon Allah?” Bai waiwaye shi ba, har ya tambaya sau uku. Ya ce “A cikinmu akwai Salmanul Farisi, sai ya dora hannunsa a kan Salmanu, sannan ya ce: “Da imani zai kasance a cikin (tauraruwar) Surayya, wasu mazaje ko wani namiji daga cikin wadannan zai dawo da shi (duniyar nan).”
Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (4)
Salmanul Farisi yana Madina a matsayin bawan Bayahuden da ya saye shi, har Manzon Allah (SAW) ya yi hijira. Bai san da batun hijirar ba,…