Salmanu ya ci gaba da cewa: “Sai na aika ga Nasaran na ce musu: “Idan mahaya masu tafiya Sham suka zo wurinku ku gaya mini. Lokacin da mahaya daga Sham suka iso, na samu labarin haka, sai na kwance daurin da aka yi mini, na fita tare da su a boye har na yi nisa a kan hanyar zuwa Sham.”
Salmanul Farisi (Allah Ya kara masa yarda) ya yi hijira a tafiyarsa ta neman shiriya da gano hakikanin gaskiya. Ya yi hijira ya bar iyalinsa da kasarsa da jin dadin duniya da ni’imarta. Domin duk wanda yake son ni’ima dole ya bar wata ni’imar. A yau a cikinmu wane ne ke son ya bar ni’imar duniya domin neman ni’imar Lahira? Wane ne zai iya fita daga kasarsa ya rabu da iyayensa da ’yan uwansa domin neman shiriya da gano hakikanin gaskiya?
Wannan somin tabi ne na doguwar tafiyar gano gaskiya da Salmanun Farisi (RA) ya yi. Wannan somin tabi ne na wahalar da ya fuskanta a tafiyarsa ta gano gaskiya.
Salmanu ya ci gaba da labarta mana wannan tafiya tasa inda ya ce: “Lokacin da na isa Sham, sai na ce: “Wane ne mafi falala da ilimin wannan addini?” Sai suka ce min: “Fadan Majami’a.” Sai na isa gare shi. “Na ce: “Lallai ne, ni, hakika na yi kwadayin wannan addini na Nasara, saboda haka ina so in kasance tare da kai. Zan rika yin hidima a majami’arka ina karatu a wurinka, ina ibada tare da kai.”
Da wannan ne tafiyar Salmanu ta neman shiriya da haske ta fara. Salmanu ya zauna har ya gano cewa lallai Fadan nan mugun mutum ne, yana umartar mabiyansa da bayar da sadaka (baiko), idan aka ba shi dukiya domin ciyar da ita saboda Allah sai ya taskace ta domin amfanin kansa, ba ya ba fakirai da matalauta komai daga cikinta.
Salmanu ya ce: “Sai na tsane shi mugun tsana, saboda abin da na ga yana yi. Sai wannan Fada ya mutu. Sai Salmanu ya ce da mabiyansa, “Lallai wannan mutumin naku mugun mutum ne. Yana umartarku da sadaka, yana taskace ta domin amfanin kansa, sai ya nuna musu inda ya taskace dukiyar.”
Suka fito da ita dimbin zinari da azurfa, da suka gan ta, sai suka ce wallahi ba za mu rufe shi ba, sai suka gicciye shi suka yi rajamu ga gawarsa da duwatsu. Nasaran suka kawo wani mutum suka dora shi a gurbinsa.
Salmanu ya ce: “Sai na zauna da shi, wallahi ban taba ganin wani mutum da ya fi shi gudun duniya, ya fi shi kwadayin Lahira kuma ya fi shi naci wajen ibada dare da rana ba.”
Salmanul Farisi (RA) ya ce: “Sai na so shi, so mai tsanani. Kuma bai dade ba sai rashin lafiyar da zai yi ajalinsa ya sauka masa. Sai na ce masa: “Ya shugabana! Hakika na ga alheri mai yawa a wurinka, kuma na so ka so mai yawa, ga shi mutuwa ta taho maka, zuwa ga wane ne za ka yi min wasiyya? Wane ne wanda zan zauna da shi a bayanka?”
Sananne ne cewa kowanenmu yana bukatar abokin zama na gaskiya da aboki mai cika alkawari da tsare amana, wanda zai yi abota da shi don komawa ga Ubanginjinsa. Saboda an halicci mutum a matsayin mai rauni da bai iya tsayawa da kafarsa shi kadai, yana samun karfi ne ta dogaro da ’yan uwansa.
Don haka mai karatu ko ka taba zama ka yi tunani kan wanda ya kamata ka yi abota da shi? Kada ka yi abota da wanda halinsa ba zai karfafa ka ga komawa ga Allah ba, kada ka yi abota da wanda maganganunsa ba za su shiryar da kai zuwa ga Allah ba.
Da Salmanu ya fada wa Fada haka, sai Fada ya ce masa: “Ya dana! Wallahi ban san wani mutum da yake kan irin abin da nake kai ba, sai wani mutum a Mosul (kasar Iraki). Ka isa gare shi in za ka iya yin haka.”
Mu dubi wannan tafiya ta neman shiriya daga kasar Farisa zuwa Sham (Siriya), sannan daga Sham kuma an ce ya tafi Iraki. Kuma a lokacin babu jirgin sama ko na kasa, babu mota kai ko keke babu, daga doki sai jaki sai rakumi. Amma haka Salmanu ya shirya tafiya domin neman shiriya, ba domin fatauci ko neman kudi ba. Ya rabu da iyayaensa alhali dan gata ne, ya shiga rayuwa mai wahala da barazana, ya mayar da kansa marayar dole, domin neman shiriya! Iyayen da yake jin ya samu a hanyarsa ta neman shiriya ga shi sun koma ga Allah, ya sake komawa ga halin maraici!
Lokacin da Salmanu ya halarci jana’izar wannan Fada ana gama binne shi a kasa, sai ya ce: “Na fita daga kasar Sham na tunkari Mosul har na isa ga mutumin da aka yi min wasiyya da shi. Lokacin da na isa gare shi, sai na ba shi labarina. Na zauna a wurinsa sai na ga alheri a tare da shi. Sai dai kuma zamana da shi bai dauki dogon lokaci ba, sai wannan Fada ya rasu.”
Sai dai kafin rasuwarsa Salmanu ya ce: “Da na ga mutuwa ta bijiro masa, sai na ce: “Ya shugabana! Hakika abin da kake gani na al’amarin Allah ya zo maka, kuma ka san al’amarina, to, zuwa ga wane ne za ka yi min wasiyya?”
Tirkashi! Allah Ka rahamshi Salmanul Farisi wanda bai gajiyawa da neman shiriya. Dubi yadda yake neman komawa wurin wani malami daga wani malamin. Bai ce ilimi ya ishe shi ba, shi ma bari ya kafa nasa masallaci ko majami’a. Bai ce ilimi ya ishe shi ba, shi ma bari ya fara da’awa! A’a so yake a sake shiryar da shi zuwa ga wani mutumin kirki cikin malaman addinin da ya yi imani da shi a wancan lokaci wato addinin Nasara, domin ya ci gaba da samun shiriya.
Mu tambayi kanmu, shin malamai nawa muke bi daya-bayan daya domin neman shiriya daga gare su? Wani da ya iya Larabcin da zai iya daukar littafi ya karanta ya fassara shi ke nan ya zama Sheikh, sai ya kafa tasa da’awar ko masallacin ya tara mabiya, kila ma ya rika fassara nassoshin bisa tunaninsa ba bisa koyarwar malamai magabata ba. Ko ya rika tsanantawa a kan abin da bai kamata ya tsananta ba! Saboda ya samu ya tara nasa mabiyan domin ya kawo musu sabon al’amari da sauran malaman da suke tare da su ba su kawo musu ba.
To Salmanul Farisi ba mabiya yake nema ba, shiriya yake nema, ba suna yake nema ba, shiriya yake nema, shi ya sa duk lokacin da ya lura wannan malami yana neman mutuwa, sai ya neme shi kan ya shiryar da shi zuwa ga wani malamin da yake ganin na Allah ne.
Mai karatu ka taba tambayar malaminka a kan ya nuna maka wani malami mutumin kirki da zama da shi zai amfane ka domin ka je wurinsa daukar karatu?
Lokacin da Salmanul Farisi ya shaida wa Fada bukatarsa ta ga wa zai yi masa wasiyya, sai Fada ya ce: “Ya dana! Wallahi ban san wani mutumin da yake kan abin da muke kai ba, sai wani mutum a garin Nasibin, domin haka ka koma wurinsa ka lizimce shi idan za ka iya zuwa.”
Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (2)
Salmanu ya ci gaba da cewa: “Sai na aika ga Nasaran na ce musu: “Idan mahaya masu tafiya Sham suka zo wurinku ku gaya mini.…