✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Salmanul Farisi: Abin misali ga mai neman shiriya (1)

Godiya ta tabbata ga Allah Mai shiryar da wanda Ya so. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad wanda aiko…

Godiya ta tabbata ga Allah Mai shiryar da wanda Ya so. Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halitta, Annabi Muhammad wanda aiko shi ya zamo rahama ga dukkan halitta.
Bayan haka, a yau za mu nazarci wani abu daga tarihin fitaccen sahabin nan da rayuwarsa ta zamo haske da abin misali ga duk mai neman shiriya.
kissar rayuwarsa kissa ce da ke cike da kaunar Allah, kissa ce ta shiriya a bayan bata, kuma kissa ce ta shiriya. kissa ce da idan ka karanta ta, za ka iya yin tuba ta gaskiya, ka tsayu a kan himma madaukakiya da cikakken kwadayi na komawa ga Allah. kissa ce ta wani mutum da bai dauki rayuwarsa da dukiyarsa da kasarsa da danginsa komai ba a kokarinsa na neman shiriya. Don haka ya yi hijira daga garinsa da kasarsa da kuma danginsa.
Labari ne na wani mutum da ya dandani wahala ya yi fama da gajiya, ya hadu da wahalhalu da tsanani iri-iri a hanyarsa ta komawa ga Allah da addininSa mai girma.
Mu kalli wannan kissa mai ban sha’awa da mamaki, kissar mutumin da ya fi duk mutanen Hijaz musamman Larabawa nesa da shiriya ko samun shiriyar, ya fi su kusa da kafirci da bata.
Muhallin da yake zaune da abokan zamansa da al’ummarsa da iyalinsa da gidansa, kowannensu kira yake yi zuwa ga bata da fasikanci.
Wannan jarumi ya tashi ne a tsakanin mutanen da ba su san Allah ba, maimakon haka wuta suka sani, domin haka suke bauta mata, koma bayan Allah.
Wannan bawan Allah ya fantsama duniya, ya hadu da wahala a hanyarsa ta gano gaskiya, daga gari zuwa gari, daga kasa zuwa kasa, cikin wahala, yana bibiyar saututtukan da suke cewa: “Ka ci gaba a kan wannan gwadabe, kada ka yanke kauna! Kuma kada ka yanke kauna koda tafiyar ta yi maka tsawo.”
Zangon da za mu ci can nesa ne, kuma tafiya ce mai tsawo zuwa kasar Farisa, domin mu ga rayuwar wani jarumi daga cikin jarumanta, kuma sahabi daga cikin sahabban Manzon Allah (SAW).
Mu saurari wannan kissa daga bakin wannan jarumi wanda saboda karfin imaninsa aka ruwaito Manzon Allah (SAW) yana sanya shi cikin iyalan gidansa. Wannan sahabi shi ne Salmanul Farisi (Allah Ya kara masa yarda): Imamuna Ahmad bin Hambali (Rahimahullah) ya ruwaito kissar Salmanul Farisi a cikin Musnad dinsa kamar haka:
“Na kasance saurayi Bafarise daga yankin Isbahan daga wata alkarya da ake kira Jeyyan, mahaifina shi ne jagoranta, kuma yana daga cikin mawadatan alkarya kuma mafiya daukakarta.”
Na tabbata ba abin mamaki ne ba a ga fakiri ko miskini ko wani mai rauni ko marar gata yana tuna Allah da komawa gare shi, yana gudun duniya yana kwadayin Lahira, yana ta’allaka da wuraren neman ilimin addini da na Alkur’ani.
Abin da zai iya ba mutum mamaki, shi ne a ga wanda ya mallaki duniya ta kowane gefe, yake juyawa a cikinta yadda ya so. Daloli da Yuro da Fama-Fama suna zuwa masa ta ko’ina, Naira kuwa tsohon yayi ne, amma a iske shi ya rika sayen gidan Lahira da duniyar da ya samu, kuma ya kiyaye dokokin Allah komai nasa na bisa turbar da Allah Madaukaki Ya tsara!
To Salmanul Farisi ya kasance yana rayuwa cikin ni’ima da daula, yana cikin ’ya’yan da mahaifinsa ya fi so, babba dan manya. Yana tsakiyar fitina ta dukiya da kayan sha’awoyin duniya da rude-rudenta, yana nikaya a cikin jin dadi. Salmanul Farisi ya tashi cikin wadata da daukaka da izza.
Salmanul Farisi yana yawan fadin cewa: “Mahaifina Bamajushe ne mai bautar wuta.” Sai na yi ta kokarin neman ilimin addinin iyayena har sai da na zama mai hidimar wutar da muke bauta mata.”
Salman ya ci gaba da rayuwar Majusu na tsawon lokaci, har zuwa lokacin da Allah Ya so ya fita daga killacewar da mahaifinsa ya yi masa, daga bautar wutar gado da suka kasance manya a cikinta. Sai wata rana mahaifinsa ya aike shi zuwa wani gari da ya yi mantuwa. Salman ya ce: “Sai na fita, a kan hanya, sai na ga wata majami’a (coci) daga cikin majami’un Nasara (Kiristoci). Kuma na ji muryoyin Nasara suna Sallah (bauta/addu’a). Sai na tsaya ina mamaki. Hakika bautarsu ta burge ni, na yi kwadayin addininsu. Sai na ce: “Wallahi wannan (addini) ya fi wanda muke kai…. kuma wallahi ban bar su ba, har sai da rana ta fadi, ban je wurin aikar mahaifina ba.”
Mai karatu a matsayinka na Musulmi, ka taba wucewa ta wurin da wasu da ba fahimtarku daya ba, ko ba akidarku daya ba, ko ba kungiyarku daya ba, suke wa’azi ko wani taro na addini, ka tsaya cikin sha’awa da zuciya sakakkiya ka saurari abin da suke fada ko za ka samu wani abin karuwa? Ka taba tunanin ka yi musu tambaya ta sha’awar abin da suke kai, bayyan ka fahimci abin da suke kai din ya fi naka?  To saurari yadda Salman ya yi bayan ya fahimci cewa abin da Nasara suke kai ya fi nasu na bautar wuta.
“Sai Salmanul Farisi ya tambayi yadda ake shiga wannan addini. Sai suka ce masa: “Ka tafi kasar Sham (Siriya) domin ka koyi addinin Nasara.”
Salman ya ce: “Da dare ya yi, sai na koma ga mahaifina. Sai mahaifina ya tarbe ni, yana tambayata abin da na yi. Sai na ce: “Ya Babana! Lallai ne, hakika na wuce wasu mutane suna bauta a cikin majami’arsu, sai abin da na gani na addininsu ya burge ni. Kuma ban gushe ina wurinsu ba, har sai da rana ta fadi. Sai mahaifina ya fusata da abin da na yi. Kuma mahaifina ya ce: “Ya dana, babu wani alheri a cikin wancan addini, don haka ka rike addinin iyayenka!”
Wannan shi ne halin iyaye da dama, kuma Alkur’ani ya yi ta nuni kan hakan a wurare da yawa game da irin wannan hali nasu: “Lallai ne, mu iske iyayenmu a bisa wani addini, kuma lallai mu a bisa gwadabensu masu shiryuwa ne.” Ba su kwadayin waninsa komai kasancewarsa gaskiya.
Salmanul Farisi ya ce: “Na ce, a’a, wallahi Ya Babana! Lallai shi ne mafi alheri daga addininmu. Sai mahaifina ya tsorata da abin da na fada, ya ji tsoron kada in bar addininsa na Majusanci na bautar wuta. Sai ya kulle ni a gida, ya sanya min sarka a kafafuna biyu ya daure.”
Mahaifinsa ya daure shi ya sanya masa takunkumin tattalin arziki, ya rusa daukakarsa, ya takura sha’awarsa ta samartaka, saboda tsoron kada ya bar addininsa, sai dai kuma bai iya takurawa ko kayyade ko daure zuciyarsa game da shaukin da yake da shi zuwa ga Allah ba!
Zuciyar Salman (RA) ta yi kunci kana bin da mahaifinsa ya yi masa, ya rika jin ya zama bako a cikin gidansu, bako a tsakanin iyalansu, kuma bako a tsakanin abokansa.