Lado (ba asalin sunan shi ba) wani sanye da farar shadda da jar dara a gindin wata bishiya a wani filin Idi a Jihar Kaduna yana tattaunawa da abokansa suna cikin nishadi da walwala.
“Yau akwai casu mutumina,” kamar yadda wakilinmu ya jiyo ya fada.
A Musulunci, ana daure shaidanu a duk lokakin da watan Ramadan ya tsaya.
Hakan ya sa ake samun masu dainawa ko rage ayyukan alfasha, musamman a tsakanin matasa maza da mata da masu shaye-shaye.
A watan Ramadan matasa marasa ji da dama sukan zama na-gari su nutsu, masallatai su rika cika.
Mata masu yawon dandi a wasu gararen kuma, akan samu wadanda ke komawa gidajen iyayensu a watan Ramadan.
Sai dai kuma da zarar watan ya wuce, duk wadannan abubuwa kan koma yadda suke a baya, wanda ke farawa da abin da a wasu shagulgula da a wasu wuraren ake kira tarbar shaidan, da dai sauransu.
Yawanci matasa kan shirya casu a cikin daren da aka sanar da ganin watan Karamar Sallah — wani lokaci har zuwa safiya — inda ake shaye-shaye da sauran ayyukan alfasha wadanda suka kaurace wa a watan Ramadan.
A ranar Karamar Sallar baba, bayan idar da Sallar Idi, Aminiya ta samu zantawa da Lado a kan yadda za su tarbo ‘Shaidan’.
Lado cikin murmushi, ya ce, “Ka san an ce shaidan ne yake sawa a rika aikata mugayen halaye. To lokacin azumi an samu sauki. To idan an gama azumi, akan shirya casu, a je a dan cashe a wartsake.”
Da aka tambaye shi inda suka cashe, sai ya ce, “A jiya an cashe a wasu wurare a Maraban Jos da ke Kaduna. An cashe sosai, alhaji.
“Da muka bar Maraba, sai muka je Unguwar Barnawa, inda muka je wani waje aka ci gaba da rakashewa har tsakar dare.
“Akwai wuraren casu da yawa da Sallah. Iya karfinka ne kawai.”
Da aka tambaye shi game da ’yan mata, sai ya ce, “Ai komai akwai a wuraren nan. Da ‘yan matan da kayan shaye-shaye.”
Lado wanda DJ ne, ya ce haka lamarin yake dama a duk tsakanin matasa irinsu, idan suna murnar Sallah.
Ya kara da cewa, “Wasu ne suke cewa za su je tarbo shaidan din kawai amma da wasa suke.”
A wani bangaren kuma, Aminiya ta ci karo da wata wadda aka sakaya sunanta a Kaduna, wadda take tafiya ta dade ba ta gari, amma da zarar Ramadan ya zo sai ta dawo.
Kokarin tattaunawa da ita ya ci tura, amma wani wanda ya san ta sosai ya ce haka take yi duk shekara.
“Ta fi zama a Abuja, amma duk Sallah tana dawowa a gida. Abin mamaki kuma duk idan ta zo da Ramadan da ita ake zuwa karatun Qur’ani da Asham da tahajjud duka.
“Kuma kullum tana cikin hijabi. Sai dai kuma bayan Sallah sai ta koma ruwa.
“Muna addu’a Allah Ya shirya ta, Ya shiryar da mu baki daya.”