Gwamnatin Jihar Kano ta ba da hutun kwana 10 ga makarantun firamare da na sakandare, na gwamnati da ma masu zaman kansu, albarkacin bikin Babbar Sallah a Jihar.
Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Laraba ta hannun kakakin Ma’aikatar Ilimin Jihar, Aliyu Yusuf, gwamnatin ta bukaci iyayen yara su sani cewa hutun zai kankama ne daga ranar Alhamis, bakwai zuwa Lahadi 17 ga Yulin 2022.
- Saudiyya ta kori shugabannin kamfanin kula da alhazai
- Zargin Batanci: Lauyan Abduljabbar ya fice daga kotu a fusace
“Don haka, Ma’aikatar Ilimi ta ba da umarnin dukkan dalibai masu rubuta jarrabawar NECO da NABTEB da kuma NBAIS hade da daliban da suka zo daga wasu jihohi da ke makarantun GSS Gwarzo da GGSS Shekara, su zauna a makarantunsu.
“Kazalika, ma’aikatar ta umarci shugabannin makaratun su tabbatar dalibai masu kwana a makaranta sun dawo hutun ran Lahadi 17 ga Yuli, sannan daliban je-ka-ka-dawo a ranar Litinin, 18 ga Yuli, 2022, inda za a ci gaba da karatu ba tare da bata lokaci ba,” inji sanarwar.
A karshe, ma’aikatar ta yi gargadin za a hukunta duk wani dalibin da ya saba ka’idar komawa makaranta kamar yadda aka tsara.