An yi wa fursunoni 136 afuwa a Kano, inda Gwamna Abdullahi Ganduje ya ba da umarnin sakin su a matsayin ‘Barka Da Sallah’.
Ganduje ya yi wa fursunonin afuwa tare da ba kowannensu kudin mota N5,000 ne a lokacin da ya ziyarci Gidan Yarin da ke Goron Dutse a ranar Talata, bayan sallar idi.
“A matsayinku na ’yan Najeriya kun cancanci kulawa shi ya sa muka zo a Ranar Sallah mu taya ku murna ta hanyar sakin wadanda aka yi wa afuwa daga cikinku.
“Muna son wadanda suka tuba daga cikinku su yi alkawari cewa ba za su koma wa munanan ayyukan da suke aikatawa a baya ba,” inji shi.
Ganduje ya ce: “An saki wasu ne saboda rashin lafiya, wasu kuma sun kasa biyan tarar da aka yi musu, sai kuma wadanda aka tsare su fiye da kima”.
A cewarsa, hakan ya zo daidai da umarnin Shugaba Buhari na rage cunkoso a gidajen yari.
Kwanturola mai kula da gidan yari, Shiyyar Kano, Sulaiman T. Sulaiman ya yaba wa gwamnan bisa kyakkyawar mu’amala tsakaninsa da gidajen yarin da ke jihar.
Ya kuma yaba game da yadda ya tallafa musu da raguna da shanu domin shagalin sallah.