✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin waya

Shawara ga Shugabannin APC Shugabannin Jam’iyyar APC ta Najeriya” rike guntun Gatarinka ya fi Jiran wani ya sara, ya baka,” don mun ga kuna shirin…

Shawara ga Shugabannin APC

Shugabannin Jam’iyyar APC ta Najeriya” rike guntun Gatarinka ya fi Jiran wani ya sara, ya baka,” don mun ga kuna shirin yin watsi da Malam Shekarau da Hon. Faruku Adamu da Bafarawa, don haka Shugabannin Jam’iyyar APC ku yi hattara kada ku Kwashi ‘Kara da Kashi.’ Sannan ku bar murna karenku ya kama Zaki don Gwamnonin PDP 7 da kuke hasashen Komarwarsu APC to Ku sani fa akidarku ba daya bace don haka hausawa dai sun ce iya ruwa fidda Kai, sannan da muguwar rawa gara kin tashi.
Daga Zaidu Bala Kofa Sabuwa Birnin Kebbi, Jihar Kebbin Najeriya. Gsm 07037697009.

Ga Jam’iyyar APC
Jam’iyyar APC ku shirya karbar mulki da izinin Allah. Daga Sani abdu Beta 07068223015.

Ga Goodluck
Don Allah Aminiya ku isar min da sakona ga Shugaban kasa Jonathan ya hakura da takara, ya kawo Manjo Al-Mustapha ya ba shi. Daga Ibrahim JG. 08037425125.

Ga ’yan PDP
Salam Aminiya wannan rigima ta PDP Allak ka kara fadadata ta fi haka tsanani; Allah kar ka hada kansu. Idan kuma masu shiriya ne, Allah Ka shirye su; idan kuwa ba masu shiriya ba ne, Allah Ka tsaremu daga sharrinsu. Daga Adamu Suleiman Kaugama 08037015766. Ina mika gaisuwata ga dukkan ma’aikatan wannan kamfani ta jaridar Aminiya da kuma wannan fili mai albarka. Daga Sani Abdu Beta 07068223015.

Kira ga Hukumar KASROMA
Salam don Allah gwamna Shema kamar yadda ka zgaye birnin Katsina da ‘Ring Road’ ya yi fes ake tag ode maka, to muna fatan za ka umarci KASROMA da ta gyara mana hanyar da ta gyara mana hnayar da ta tashi daga sabuwar kofa ta bi ta lambobi ta bille Dutsin Safe Lowcost. Daga Mustapha Idige, Mataimakin Babban Jami’in Medecins Sans Frontieres, France 081699583500.

Ta’aziyyar ma’aikacin Daily Trust
Inna Lillahi wa inna ilaihir Raji’un. Edita ina mika sakon ta’aziyyar ma’aikacinku da ya yi shahada, wato Malam AbdulWasi’u. Allah Ya jikanshi, amin summa amin. Daga Adamu Mamman Suka 07066018903.

Ta’aziyyar Lawal baidu
Inna Lillahi wa inna ilaihir raji’un. Allah Ya jikan Lawal baidu, Ya gafarta masa, ya sanya shi cikin Aljanna madaukakiya. Kuma Ya ba mu hakurin juriya. Amin. Daga Isa Murtala Gamagira, Sashin Kula da lafiya matakin farko (PHC), Soba, Maigana Jihar Kaduna. 08135419744.

Ga ma’aikatan Aminiya
Salam ga ma’aikatan Aminiya, Allah Ya kara muku daukakar aiki. Ya kamata ku bibi kasuwar gwanjo da ta bude a nan Kaduna saboda shigowar sanyi. Daga Ado M. Garba Kibiya 08051534212

Ga danmajalisar Bakori/danja
Edita don Allah ka isar da sakona wai makala nufi da mu ne ka tafi Abuja, ka manta da wadanda kake wakilta, kuma har kake ikrarin kai kana yi wa mutanenka adalci. Daga DD Umar danja 08032490360.

Ga Gwamnonin G7
Assalamu alaikum don Allah Edita ka mika mini shawarata ga ’yan G7, indai don talaka suke yi, to za mu gani in koma don kansu suke rigimar za mu gani, amma su sani mu talakawan Najeriya, mun zuba musu ido. Allah Ya taimaki talakawan Najeriya amin. Daga M.D. Sani Bararo, Kano Hausawa 08038492252.

kalubalenku ’yan Najeriya
Salam zuwa ga Aminiya, to ’yan Najeriya kalubale a garemu, yau ga shi Shugaban kasar nan ya sanya wa gwamnonin Arewa takunkumi, saboda wata bukata tasa da suka ki amincewa da ita. Daga Sani Mai Jarida Dawaki 07030274337.

Ta’aziyyar ’yan Jarida
Ina mika ta’aziyyata ga kungiyar ’yan jarida ta kasa da ma duniya baki daya a kan rasa ’ya’yanta da tayi a kasar Mali da fatan Allah Ya jikansu amin. Daga Ibrahim KSD 08031944943.

Gwamnatin ’yan uwa
Zilkifilu Amfani Zariya ya ce Gwamnatin Kaduna ta ’yan uwa da abokan arziki ce. Ashe duk kanwar ja ce, daga kasa har sama. Sauran jihohi kasar nan, abin da suke fama da shi ke nan. Haka kuwa shi ke hana kasar nan zama lafiya. Daga Mamman Lawan Gashua 07010409541.

Ga mayaudaran’yan mata
Assalamu alaikum, Aminiya a kowane lokaci ina tare da ku. Ku taimaka ku kara tura wannan sakon ga mayaudara ’yan mata. Daga AbdulMumin Abubakar Zamfara 08143114865.

Ga mallamai
Sallam. Aminiya gatan kowa, don Allah ku mika sakona ga mallamai. Ku ji tsoron Allah, ku daina yaudarar al’umma. Daga Suleiman Hamisu Inuwa 08036940567.

Ga mazaunan Kubwa
Salam Edita ya aiki? Ga sakona zuwa ga ’yan Abuja mazauna Kubwa, ’yan Magana suka ce ‘jiki amgayi,’ ku zabi Jonathan ga shi yana saka muku da zaben da kuka yi, ya turo ana ta rushe muku shaguna da gidaje. Don haka jiki magayi,’ a zabe naga sai ku sake. Daga Bash M. Mubi 08062673050.

Ga Solomon Darlung
Salam Edita Aminiya jinjina ga Barista Solomon Darlung, abin da ka yi a Jos da Minna wajen jin ba’asin jama’a na taron kasa ya yi daidai. Haka ake so gwarzon namiji, don irin su Farfesa Gana da kungiyoyin su suke kasha jama’a, inda gwamnati ke amfani da su wajen cin karanta ba babbaka. Daga Rabi’u Baba Lawal Funtuwa 08153171016.