✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sakonnin waya 1

Ga Sarkin Minna BahagoAssalamu alaikum. Edita don Alllah ka ba ni dama in mika sakon taya murna ga sarkinmu mai adalci, Alhaji Dokta Umar Faruk…

Ga Sarkin Minna Bahago
Assalamu alaikum. Edita don Alllah ka ba ni dama in mika sakon taya murna ga sarkinmu mai adalci, Alhaji Dokta Umar Faruk Bahago, kan cikarsa shekara 25 a karagar mulkin Minna. Allah Ya ja zamanin sarki. Daga Maman Innawuro, Tunga Minna 07030891275.

Shugaba Jonathan a duba dimokuradiyya
Ma’anar dimokuradiyya ita ce ’yanci da kuma ’yancin fadar albarkacin baki. Shin haka ne a kasata Najeriya? Ina kira ga Maigirma shugaban kasa ya duba wannan al’amari. Mayakinsa kuma jigo a PDP, wanda ya sadaukar da rayuwarsa, ya tabbatar sun dora Jonathan a kujerar shuaban kasa, wato Sule Lamido. An kira shi da sunaye iri-iri, kafiri. Amma da dai sauransu. Shin don ya fadi ra’ayin sa sai a tsane shi? Har ma abin ya wuce kansa, ya wuce kansa ya kai ga iyalansa. Kuma shugabanci bay a yiwuwa said a hakuri. Daga Hansa’u Hussaini Girbobo 07054956908. Nasiha ga Shugabannin Najeriya
Assalamu alaikum zuwa ga shugabannin Najeriya ku ji tsoron Allah kotuna wata rana Allah zai tambayi abin da kuka aikata. Daga Yusuf Haruna Ummar  08139618011.

Hattara PDP
A Jihar Sakkwato mun yi jana’izar muguwar jam’iyya, mun dawo gidan asali, mun nemi afuwar maigida , kuma ya yafe, wato Attahiru Bafarawa, garkuwan Sakkwato. Daga Bagudu Baja da Musty APC sak 08034068363.

KAROTA ta addabi Musulmi
Assalamu alaikum Aminiya. Ana cewa Gwamnatin Jihar Kano tana aiki, to ga watakila ’yan KAROTA ka ga yadda ga baki daya suka hana Musulmi hulda kama daga kasuwancin da aka san Kano da shi. Daga Sani Plaza Kano 08137692927/08189023149.

Ga Sabuwar PDP
Babangida da Sule Lamido kun nuna mana kuna jin tsoro a kan tafiyar sabuwar PDP idan ba za ku iya ba, to ku koma wajen Goodluck ku ce kun daina adawar mana. Daga 07038752013.

Ga Gwamna Wamako
Aminiya don Allah ina son ku yi kira ga Gwamnan Jihar Sakkawato, Aliyu Wamako ya taimaka ya biya wadanda suka yi ritaya, domin wasu har sun mutu ba su karbi hakkinsu ba. Ka tausaya gwamnan adalci. APC sak. Daga Malam Kabiru Hamdala Gusau GRA 08066272283.
    Ga ’yan sandan Najeriya
’Yan sandan Najeriya. Ku daina kama barayi in sun yi sata, saboda akwai shugabanni a Najeriya da ke taba kuruciyar bera. Idan masu shiryuwa ne Allah Ya shirye su; idan kuwa ba za su shiryu ba, Allah Ya tsare al’umma daga sharrinsu. Amin. Daga Zainab (MAMI) Gombe 08062906565.

Maraba da Gwamnonin PDP
Assalamu alaikum. Muna amraba da zuwan gwamnonin PDP bakwai cikin jam’iyyar APC. Daga Lawal Adda Unguwar Yelwa Lafia, Nasarawa. 08135634634.  

Ga Gwamnan Al-Makura
Aminiya Allah Ya s amuku albarka, rokona zuwa ga Gwamnan Nasarawa, Alhaji Tanko Al-Makura a kan hanyar Panda, wadda ta fara kafin ya hau kujerar gwamna, ya yi kokari ya gama mana kafin zaben 2015. Ina kuma roko akwai masu kwashe yashi suna bata hanya da an gama ya taimaka ya tura ’yan sanda, su kama wadannan mutane. Na gode. Daga Joseph Musa Panda.  08076239333.

Ga Sufeto Janar
Salam Edsita ina so ka mika min sakona zuwa ga Sufeto Janar na ’yan sandan Najeriya, da ya duba dambarwar da take sakanin ‘’yan sandan Jihar Kano da iyalan Hassan Alfa, wanda aka ce dukan da suka yi masa, shi ne sanadiyayr rasuwarsa. Allah Ya kyauta. Daga Alassan Ala 08055023966.
Gwamna Shema ka yi bincike
Aminiya ’yar amana don Allah ku mika mana kira ga Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shema. Don Allah ya binciki yadda ake aiwatar da ayyuka a karamar Hukumar danja, domin kwanakin baya daya daga cikin wakilanka, Musa Ladan ya ce Gwamnatinka ta gina wasu hanyoyi a danja da kewaye, a wadannan hanyoyin wallahi gwamna da ake cewa an yi ba dayar da aka taba. Daga Musa Unguwar Mai Yasin, danja, Jihar Katsina 08155648155.

Shugaba Jonathan a duba dimokuradiyya
Ma’anar dimokuradiyya ita ce ’yanci da kuma ’yancin fadar albarkacin baki. Shin haka ne a kasata Najeriya? Ina kira ga Maigirma shugaban kasa ya duba wannan al’amari. Mayakinsa kuma jigo a PDP, wanda ya sadaukar da rayuwarsa, ya tabbatar sun dora Jonathan a kujerar shuaban kasa, wato Sule Lamido. An kira shi da sunaye iri-iri, kafiri. Amma da dai sauransu. Shin don ya fadi ra’ayin sa sai a tsane shi? Har ma abin ya wuce kansa, ya wuce kansa ya kai ga iyalansa. Kuma shugabanci bay a yiwuwa said a hakuri. Daga Hansa’u Hussaini Girbobo 07054956908.

Jaje ga Jonathan
Aminiya ku taimaka ku ban dama in isar da sakona ga Shugaba Jonathan don in yi mashi jaje da rashin lafiya da ya yi fama da ita. Allah Ya ba shi sauki, amin da koshin lafiya. Daga Alhaji Kankat Arawa Jihar Gombe 07085604839/07061316464.

Ga masu addu’ar jaraba
Editan Aminiya don Allah ka isar min da sakona ga wadanda suka taya ni da addu’a, har na samu damar cin jarraba, kuma kiredit tara. Daga kanwar Mai Kawo Kano 08090852785.

Ta’aziyyar Barista Yahaya Mahmud
Allah Ya jikanshi da rahama, Ya sa aljanna ce makomar shi. Mu kuma idan tamu tazo Allah Yasa mu cika da kyau da imani Ya kyautata karshenmu. Daga AbdurRashid Ahmad Mustapha Birnin Gwari 08167671842.