✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sake karfafa koyar da addini a makarantu

Kwanakin baya ne Majalisar Sarakunan Gargajiya ta kasa (NCTRN) ta kammala babban taronta karo na shida a Sakkwato inda ta yi kira ga gwamnati ta…

Kwanakin baya ne Majalisar Sarakunan Gargajiya ta kasa (NCTRN) ta kammala babban taronta karo na shida a Sakkwato inda ta yi kira ga gwamnati ta sanya nazarin addini ya zama tilas a makarantun sakandaren kasar nan.
Sarakunan sun kuma nemi a sake dawo da koyar da tarihin jama’ar kasa a makarantun. Majalisar tana karkashin shugabancin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Oni na Ife Oba Okunade Sijuwade ne. A cikin takardar bayan taro ta koka kan abin da ta kira gazawar manhajar ilimi na ta magance muhimman matsalolin kasa, tare da bayyana cewa gazawar ce ta kawo karuwar rashin aikin yi da talauci da kalubalen tsaro. Domin fara magance matsalar sarakunan sun bukaci Gwamnatin Tarayya ta sanya koyar da ilimin addini ya zama dole a matakan sakandare. Shirin Ilimi na kasa na yanzu ya sanya nazarin addini ya zamo tilas ne a shekara tara na matakin farko. An yi watsi da shekaru mafiya muhimmanci da suka hada da makarantar babbar sakandare.
Sarakunan sun nuna wannan damuwa ce bisa bukatar da ke akwai na a cike wannan gibi; kuma suna da gaskiya. Koyar da addini da ke kunshe a tsarin koyarwa manufarsa cusa wa yara kyawawan dabi’u da halaye da suka dace da al’adu da dabi’un al’umma. Wannan domin a tabbatar da sun tafi da irin akidar da al’ummar Najeriya suke kai ne. Abubuwan da ke kunshe a cikin darussan addinin musamman a manyan makarantun sakandare za su taimaka wajen dakile matsalolin da yara ke haduwa da su yayin shiga shekarun balaga, ciki har da rashin girmama na gaba ko hukuma wanda yana da matukar muhimmanci wajen sanya da’a ga matasa a wannan mataki na bunkasar halittar jikinsu.
Darussan da ake dauka daga koyarwar addini kan taimaka wajen hanawa ko rigakafin auka wa aikata ba daidai ba, tare da karfafa kyawawan halaye.
Wajibi ne gwamnati ta dubi wannan matsayi na sarakuna kan wannan muhimmin batu ta hanyar tilasta koyo da koyar da addini a manyan makarantun sakandare. Kuma a yayin da kiran na sarakuna ya cancanci goyon bayan kowa saboda muhimmancin da yake da shi ga zaman lafiyya kasa, ya wajaba a kara da cewa tilasta koyar da addini a manyan makarantun sakandare yana da muhimmanci ne kawai, amma ba shi ne ginshikin magance tabarbarewar kyawawan dabi’u da ake fama da su a kasar nan ba.
Ba wani bambancin da za a samu idan aka yi wani tsari ko aka sanya koyar da addini tilas a yayin da rayuwar daidaiku na wadanda ya kamata su nuna misali nagari wajen shugabanci suka rika sabe wa kyawawan dabi’u da halaye da al’adun jama’a.
Malamai a Najeriya kamar shugabannin siyasa galibi ba su nuna misali nagari ga matasa da kananan yara. Da yawa matasan yau da suke kallon akwatunan talabijin ko sauraron rediyo sukan ji yadda ake ba da rahoton cewa malaman makaranta sun yi fyade ga kananan yara ko yadda jami’an gwamnati suka yi almundahana da kudin jama’a ko yadda sarakuna suka zubar da martabarsu ta hanyar karkata ga wata jam’iyyar siyasa ko hulda da ’yan siyasa ko yadda iyaye suke kin kula wajen sauke nauyin kula da nuna kauna ga ’ya’yansu.
 Batun ya wuce na matsayin sanya karantar da addini a manhajar ilimi ta manyan makarantun sakandare, malamai su tsallake batun wa’azi a fatar baki. Shugabanni da sarakuna da iyaye wajibi ne su sauke nauyin da ke kansu na jagoranci da shiryyarwa. Sake dawo da koyar da tarihin al’ummomin kasa ma ya cancanci a duba. Maye gurbin tarihi a matakan sakandare kimanin shekara 30 da suka gabata da labarin al’adun kasa ya yi illa sosai wajen hana matasa sanin tarihi da yanayin al’ummun da suke kusa da su. Mafi muni shi ne halin ko in kula da matasa a yau suke nunawa ga al’adar nan ta adana bayanai. Sake dawo da koyar da tarihin al’ummun kasa zai taimaka wajen magance wasu kalubale da wannnan muguwar shawara a kawo aka cire shi daga manhajar ilimi.