✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sai an yi min cin wulakanci Maradona ke kira na —Mourinho

‌Jose Mourinho ya ce shahararren dan wasan kollon kafa, marigayi Diego Maradona baya kiransa hirar arziki sai an lallasa kulob dinsa a gasa. Mourinho, ya…

‌Jose Mourinho ya ce shahararren dan wasan kollon kafa, marigayi Diego Maradona baya kiransa hirar arziki sai an lallasa kulob dinsa a gasa.

Mourinho, ya je ta’aziyyar Maradona ne bayan Tottenham ta lallasa Ludogorets da ci 4-0 a gasar Europa, awa 24 bayan rasuwar Maradona ranar Laraba.

“Zai kirani idan aka ci kulob dina, amma baya kira na in nayi nasara”, inji Mourinho.

Ya ci gaba da cewa: “Maradona dan kwallo ne da duniya ba za ta taba mantawa da shi ba; Zan tabbatar dana ya san tarihinsa sosai, duk da cewa an haife shi bayan ya daina buga kwallo.

Na san idan dana ya haihu zai sanar da yayansa tarihin Maradona ta yadda ba za su taba manta shi ba.

Kamar [Alfredo] Di Stefano, ban taba ganin ya buga wasa ba, amma mahaifina ya sanar da ni game da shi, kowane zamani yana da irin nasa yan wasan, yan wasan zamanina su ne wadanda kowa ya sani.

Na yi rashin Diego. Na yi bakin cikin rashin samun lokaci mu hadu da shi mu san juna sosai yadda na so. Sai dai kuma iyalansa da abokansa da abokan aikinsa sun samu wannan damar zama da shi sosai.

Na san shi sosai saboda a duk lokacin da aka yi mini cin wulakanci zan ga kiransa amma idan na yi cin wulakanci baya kira na, ba zai kira ni ba.

Ina matukar alhinin mutuwarsa. Ina cikin damuwa tare da murmushi saboda yana sanya ni dariya a duk lokacin da muke magana da shi, inji Mourinho.