Shugabannin jam’iyyar APC na ta karyata juna game da jingine dakatarwar da suka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole a mazabarsa, da ta yi sanadiyyar barinsa kujerarsa.
Mutum 17 daga cikin ‘yan Kwamitin Zartarwar jam’iyyar 27 na Mazaba ta 10 a Karamar Hukumar Etsako ta Yamma a jihar Edo da ma na jiha, sun ce sun janye dakatarwar, tare da kiran sauran matakai su dawo wa Oshiomhole dukkan hakkokinsa na Shugaban jam’iyya na kasa, amma shugaban jam’iyyar na mazabar da kuma karamar hukuma sun karyata su.
Sakataren mazabar Emuakemeh Sule, ya gabatar wa Hedikwatar jam’iyyar abin da ya kira takardar bayan taro da ya ce, bayan nazarin dakatarwar, Kwamitin Zartarwar ya fahimci cewa “Zargin da ake masa babu tushe, sannan babu adalci a hanyoyin da aka bi wurin dakatar da shi. Don haka mun janye dakatarwar”, inji shi.
Har yanzu tsugune ba ta kare ba ke nan a rikicin shugabancin jam’iyyar mai mulki wadda kuma ke shirin zaben fidda dan takarta a zaben gwamnan Edo, inda shugabanninta na jihar ke neman jefa uwar jam’iyyar cikin rudani game da matsayin shugabancinta na kasa.
Uwar jam’iyya ta samu takardar
Yayin karbar takardar, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar (Kudu-maso-Kudu) Hilliard Eta, ya yaba wa shugabannin mazabar kan matakin wanda ya ce ya dace da kundin tsarin mulkin jam’iyyar.
- Shugabannin APC sun janye dakatarwar da suka yi wa Oshiomhole
- Kotu ta kara dakatar da Oshiomhole daga shugabancin APC
- Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi ya zama shugabanta
Prince Hilliard Eta wanda shi ne mukaddashin Abiola Ajimobi da jam’iyyar ta nada bayan dakatar da Oshiomhole ya ce hedikwatar jam’iyyar ta samu kwafin takardun amincewar kamitin zartarwa na Karamar Hukumar Etsako ta Yamma, dauke da sa hannun shugabanta Abubakar Akokia da sakatarensa Hon. Dauda Ahmed.
“Mun kuma samu na Kwamitin Zartarwan Jihar Edo wanda shugaban riko Kanar David Imuse (murabus) da Sakatare Laurence O. Oka suka sa wa wannu”, inji shi.
Kanzon kurege ne, inji shugaban mazaba
Sai dai kuma shugaban jam’iyyar APC na mazabar, Oshawo Stephen ya musanta janye dakatarwar da suka yi wa Oshiomhole daga jam’iyyar.
Shi ma shugaban APC na Etsako ta Yamma, Ezolomhe Rabiat, ya ce babu wata magana da aka yi na watsi da dakatarwar a aka yi wa Oshiomhole.
Shugabannin biyu sun ce har yanzu ‘yan Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar da aka zaba a matakan biyu a 2018 su ne halasatattu kuma babu wanda ya maye gurbinsu ba.
- Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi ya zama shugabanta
- Rudani: ‘Sabon shugaban’ APC ya soke tsarin jam’iyya kan zaben Edo
- Rikicin APC: Na koyi darasi – Adams Oshiomhole
A ranar Laraba ne dai Oshiomhole ya bar kujerar tasa bayan Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta tabbatar da hukuncin dakatarwar da Babban Kotu ta yi masa tun da farko.
Daga lokacin zuwa yanzu, an yi ta ganin juyin waina iri-iri a kan kujerar Oshiomhole wadda yake kokarin kokmawa kai, yayin da wasu bangarori a cikin jam’iyyar ke kokarin darewa a kanta.
Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da dakatar da shi ne kamar yadda babban kotun tarayya ta yanke hukunci tun da farko sakamakon dakatarwar a shugabanin mazaba suka yi masa, kan wasu zarge-zarge.
Rikicin APC ya kara kazancewa
Rikicin APC a ‘yan kwanakin nan ya yi saurin jujjuyawa tun bayan dakatarwar ta ranar Laraba, wadda ya sa a cikin dare uwar jam’iyyar ta ayyana Mataimakin Shugabanta na Kasa (Kudu), Abiola Ajimobi a matsayin mukaddashin shugaba.
Washegari kuma Mataimakin Sakataren Kam’iyyar Victor Giadom ya ce da ma can shi ya kamata ya hau kujerar kuma yanzu ya dare a kanta, yana mai cewa tun a ranar 16 ga watan Maris Mai Shari’a Samira Bature ta ba shi izinin shugabantar jam’iyyar, a shari’ar Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Kasa Mustapha Salihu ya shigar na bukatar hakan.
Sa’o’i kadan bayan nan kwamitin gudanrawar ya karyata Giadom, lamarin da ya sa Mustapha komawa kotun a ranar ya kuma samo wa Giadom izinin ci gaba da zama shugaba na riko na kwana 14 bayan bayan takadar da Oshiomhole.
- Rudani: ‘Sabon shugaban’ APC ya soke tsarin jam’iyya kan zaben Edo
- Jam’iyyar APC ta nada Ajimobi ya zama shugabanta
Mustapha ya nemi a kara tsawaita wa’adin Victor Giadom ne, wanda tun a hukuncin kotun na farko kotun ta ce ya ja ragamar jam’iyyar, muddin ba Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar ne ya yanke hukunci sabanin hakan ba.
Giadom ya soke zaben fitar da dan takaran jam’iyyar na zaben gwamnan Edo, ya kuma sanar da cewa zai gudanar da sabo. A ranar Juma’ar ce reshen jam’iyyar ne Edo ya yi fatali da kwamitin da uwar jam’iyyar ta kafa na zaben fidda gwanin. Ana ganin hakan ya zo daidai da bukatar Giadom da iyayen gidansa.
A ranar Asabar wata kotu a jihar Ribas, mahaifar Giadom ta umurce shi da ya daina gabatar da kansa a matsayin shugaban jam’iyyar. Ko kafin nan, wasu kusoshin jam’iyyar sun ce ya dade da sarayar da damarsa ta zama dan kwamitin jam’iyyar na kasa, balle har ya kai ga kujerar da yake ikirarin ya gada.
Duk zaben 2023 ake yi wa
Kazancewar rikicin shugabancin jam’iyyar tsakanin bangarori masu adawa da juna ke ikirarin shugabantar ta na da alaka da shirin zaben 2023.
Giadom na da goyon bayan kungiyar gwamnonin jam’iyyar da wasu tsoffin gwamnoni da ke shirin tsayar da dan takara a zaben 2023, yayin da Ajimobi ke da goyon bayan Kwamitin Gudanarwarta ta kasa da kuma madugun jam’iyyar Bola Ahmed Tinubu wanda shi ma ake cewa yana da muradin takara kuma suke dasawa da Oshiomhole.
Wani karibi a kungiyar gwamnonin ya ce, “Da ma Osiomhole ne babban tarnakin jam’iyyar, yanzu kuma babu shi.
Game da rikicin jihar Edo da yadda jam’iyyar ta hana gwamna Godwin Obaseki tsayawa takara har ta kai ga ya fice daga jam’iyyar, ya ce, “Mun ‘yi amannar cewa akwai hakki a kanmu na mu kare takwaranmu, Gwamna Obaseki saboda babu laifin da ya yi.
“Yanzu da babu shi [Oshiomhole] duk masu ikirarin su ne masu jam’iyya jikinsu ya yi sanyi.
“Gwamnoni za su samu yadda suke so tunda su ke da talakawa”, inji sh.
Da’awar Giadom kan shugabancin jam’iyyar
Giadom ya ce dogaro da hukuncin kotu, yanzu shi ne shugaban jam’iyyar na kasa, sannan ya sanar da cewa za a yi sabon zaben tsayar da dan takarar gwamnan Edo da Ondo, ga duk masu bukata.
Ya kuma ce nadin Ajimobi haramtacce ne kasancewar umurnin kotun da Mai Sharia Samira Bature ta bayar cewa [shi Giadom] ya zamo shugaban jam’iyyar a ranar 16 ga Maris, a shari’a mai lamba FCT/HC/M/6447/2020 na nan tana aiki.
“A lokacin dokar ba ta fara aiki nan take ba saboda daga kafar da Oshiomhole ya samu daga Kotun Daukaka Kara.
“Yanzu da kotun ta janye daga kafar kuma, ba zai yiwu mu bar gibi ba, ba ni da zabi face in sanar da ku cewa na fara aiki a matsayin shugaban riko na jam’iyyarmu, kamar yadda kotu ta bayar da umurni,” a cewarsa.
Kwamitin Gudanarwa na Kasa ya kalubalanci Giadom
‘Yan mintoci bayan sanarwarsa sai ‘yan Kwamitin Gudanarwa suka kalubalance shi, suka kuma tabbatar da nadin Ajimobi a matsayin shugaban riko.
15 daga cikin mambobi 21 kwamitin da suka sanar da hakan sun kuma ayyana Mataimakin Shugaban Jam’iyyar (daga yankin Kudu-maso-Kudu), Hilliard Eta a matsayin mukaddashin Ajimobi, wanda suka ce “dole ta sa ba ya nan”.
Ajimobi na kwance fiye da mako biyu an killace shi saboda cutar coronavirus.
Giadom ya sauka daga mukaminsa
A jawabinsa ga ‘yan jarida, Prince Eta ya ce Giadom ya dade da sauka daga mukaminsa a Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar domin yin takarar mataimakin gwamnan jihar Ribas.
Ya kara da cewa har yanzu reshen jam’iyyar na Kudu-maso-Kudu bai riga ya cike gurbin ba kamar yadda yake a tsarin mulkin jam’iyyar.
Prince Eta ya yi nade-nade
Eta ya kuma sanar da nada kwamitin gudanar da zaben fitar da dan takarar jam’iyyar a zaben gwamnan Edo na ranar 22 ga watan Yuni, karkashin Gwamna Hope Uzodinma na Imo. Ya kuma kafa Kwamitin Daukaka Karar Zaben Dan takara karkashin jagorancin Farfesa Mutapha Bello.
Sannan ya sanar da amincewa da Hon. Igo Aguma a matsayin Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar a Jihar Ribas mahaifar Giadom, har a yi babban taron zaben shugabanni a dukkan matakai a jihar.
Jam’iyyar ta ce hakan ya biyo bayan hukuncin wata Babbar Kotu a baya-bayan nan da ya tabbatar da Aguma a matsayin shugaban jam’iyyar APC na rikon jihar.
Oshiomhole zai daukaka kara
Yayin da ake cikin haka, Oshimhole ya ce yana tattaunawa da lauyoyinsa domin su daukaka kara a kan dakatarwa da aka yi masa zuwa Kotun Koli.
Oshiomhole ya ce ayyana kansa da Giadom ya yi a matsayin shugaban riko zalunci ne da rashin ladabi ga Kwamitin Gudanarwa na Kasa da ya riga ya yanke hukunci kan zaben fitar da dan takarar gwamnan Edo.
Ya kuma zargi wasu da kokarin kawo rudani a cikin jam’iyyar domin biyan bukatar kansu.
Ajimobi ya bukaci a mayar da kube
Shi kuma Ajimobi ya fitar da sako daga kan gadon asibiti yana kira da a zauna lafiya a jam’iyyar, wadda ya ce za ta kira taron Kwamitin Zartarwartsa domin shawo kan matsalolin.
“A zauna lafiya har sai mun kira taron Kwamitin Zartarwa domin lalubo mafita,” inji sanarwar da kakakinsa Bolaji Tunji ya fitar.
Ajimobi ya zama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC (Kudu) ne a wawanta Maris bayan an samu gibi bayan mai kujerar, Niyi Adebayo ya zama minista.
Jihohi biyar daga cikin shida na yankin Kudu maso Yamma (Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo) sun amince da nadin nasa.
Babbar Kotun Tarayya ta tabbatar da nadin wanda jihar Ekiti ke kalubalanta.
Shari’ar Ajimobi na gaban kotu
Da aka tuntube shi game da nadin Ajimobi, Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ekiti Barista Paul Omotoso ya ce ba zai yi magana ba domin shari’ar kalubalantar nada shi mataimakin shugaban jam’iyyar na gaban kotu, kuma za a ci gaba da shi ranar 25 ga watan Yuni.
Lauyoyin daya daga cikin masu neman kujerar mataimakin shugaban jam’iyya (Kudu) Akinyele Micheal sun gargadi jam’iyyar kar ta amince da nadin Ajimobi a matsayin shugaban riko.
Sun aike wa jam’iyyar wasika cewa kotu ba ta riga ta yanke hukunci ba tukuna, kan karar neman ta umarci jam’iyyar ta cike gurbin Mataimakin Shugaba (Kudu) daidai da kundin tsarinta.
Magoya bayan Tinubu na cikin damuwa
Rahotanni sun nuna wannan saba ta, juya tan ya haifar da damuwa a tsakanin magoya bayan Tinubu, wanda ake ganin shi ke jan akalar Oshiomhole.
Dakatar da Oshiomhole ya sanyaya gwiwar bangaren, amma daga bisani nadin Ajimobi ya kawo masa nutsuwa, saboda kusancin da ke tsakanin Ajimobin da Tinubu, wanda ake ganin yana son tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.
Wani kaulin na cewa da goyon bayan Tinubun aka nada Ajimobi a sabon mukamin.
“Daga karshe dai hankalinmu ya kwanta kasancewar duk yadda ta juya sha ne ga bangaren Tinubu”, inji wani dan cikin gida.
Wakilinmu ya tuntubi kakakin APC na jihar Legas Seye Oladejo ka lamarin, amma ya ce reshen na tare da matasyin da Kwamitin Gudanarwa kan lamarin.