✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon tsarin canjin kudi zai bunkasa kasuwannin bayan fage ne kawai – Shugaban ‘yan canji

Ba da dadewa ba, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da wasu ka’idoji ga masu hada-hadar canjin kudi, inda aka bukaci su kara karfin jarinsu…

Ba da dadewa ba, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da wasu ka’idoji ga masu hada-hadar canjin kudi, inda aka bukaci su kara karfin jarinsu daga Naira miliyan 10 zuwa miliyan 35, sannan su biya wata miliyan 35, wadda karin ruwa a cikinta; za dai a ajiyeta a matsayin kudin garkuwar asara. An kuma gindaya wa’adin cika wadannan sharuda nan da ranar 15 ga watan Yulin 2014. A wannan tattaunawar da aka yi da Shugaban Masu Hada-hadar Canjin Kudi ta Najeriya (ABCON), Aminu Gwadabe, ya soki lamirin takaitaccen wa’addin, inda ya yi nuni da cewa idan har babban banki ya ki kara wa’adin, to za a tursasa mutane da dama su bar kasuwancinsu, sannan a kara bunkasa kasuwar bayan fage. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Ka ziyarci Majalisar kasa a makon da ya wuce don gabatar da matsaya a kan sharuddan da Babban Bankin Najeriya ya gindaya wa cibiyoyin hada-hadar canjin kudi (BDC). Ko za ka yi mana bayani kan al’amuran da suka wakana?
Gwadabe: Mun je Majalisar Datijai ne don neman agajin ’yan majalisa, su taimaka mana su yi wa Babban Bankin Najeriya (CBN) magana, ta yadda za su shiga tsakanin wajen hana aiwatar da sabon tsarin da aka fito da shi.
Wadanne al’amura ne ke da matsala a jerin sababbin sharuddan da aka gindaya?
Al’amari mafi a’ala shi ne mun gabatar da makalar da ke nuna matsayinmu ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya. Mun bayyana masa cewa sabon tsarin da aka fito da shi ba shi da wata fa’ida ga masu hada-hadar canjin kudi, domin zai yamutsa al’amuran tsayayyen tsarin canjin kudi. Zai haifar da rashin aikin yi, sannan masu kasuwar bayan fage za su dawo.
Mun kuma kare kanmu  cewa masu canjin kudi ba su taimakawa wajen kassara ajiyar kasar nan a asusun kasashen waje.. Mun ce masa wannan ba gaskiya ba ce, saboda a shekarar 2012, Babban Bankin Najeriya ya sayar da Kudin musayar kasashen waje har Dala biliyan26 da miliyan 800, amma Dala biliyan biya da rabi kawai ya shiga hannun cibiyoyin hada-hadar canjin kudi (BDCs). A shekarar 2013, an sayar da Dala biliyan 33 da miliyan 300, amma Dala biliyan biyar da miliyan 300 ne kawai suka shiga hannun cibiyoyin hada-hadar canjin kudin. Sannan a watanni ukun farkon shekarar 2014, an sayar da Dala biliyan 11 da miliyan 400, amma biliyan guda da miliyan 700 ne suka shiga hannun cibiyoyin hada-hadar canjin kudin. Don haka a iya cewa kudin musaya da babban bankin ke raba wa cibiyoyin hada-hadar canjin, tun daga shekarun 2012 zuwa 2014 sai kara raguwa suke yi. Ya kuma yi nuni da cewa sana’ar mu na haifar da yawan amfni da Dalar Amurka a harkokin tattalin arziki. Mu kuwa muka bayyana masa cewa ba mu ne ke da alhakin baza kudaden a harkokin tattalin arziki ba; akwai hanyoyi da dama da ke da alaka wajen haifar da irin wadannan al’amura.
Sannan tsananin dogaro da tattalin arzikin Najeriya ke da shi, na nuni da cewa muna bukatar kudin musayar kasashen waje don shigo da kaya. Kuma tsayuwar tattalin arzikin kan turba guda, shi ya haifar da rashin ingancin kudi a wajen musaya, amma ba cibiyoyin hada-hadar canjin kudi ba.
Aminiya: A yaushe ne kuka gana da Gwamnan Babban Bankin Najeriya?
Gwadabe: Mun rubuta masa wasika a lokacin da ya kama ragamar mulki, don neman izinin kai ziyara ofishinsa, ta yadda za mu samu fahimtar juna da shi. Don haka, a Litinin din makon jiya, ya kirawo mu don ganawa da shi; washegari kuwa muka samu ganawa da shi. Mun gana da gwamna a makon da ya wuce, mun bas hi shawarwari. Sannan mun bukaci ya kara wa’adin daga 15 ga Yuli, bisa la’akari da sabon jari na Naira miliyan 35, saboda ba za a iya aiwatar da shi ba.
A lokacin da aka bukaci bankunan Najeriya su kara yawan jarinsu, an ba su wa’adin shekara biyu, su ma kananan bankuna sai da aka kara musu shekara guda suka samu aiwatar da abin da ya dace. To, mene dalilin da ya sa za a bukaci cibiyoyin hada-hadar canjin kudi su kara karfin jarinsu zuwa Naira miliyan 35 cikin makonni biyu. A ganinmu wannan bai dace, kuma ba zai yiwu ba.
Mun kuma sanar da shi cewa, ba ma karbar ajiyar kudi, bankuna ke gudanar da wannan aiki. Mun nuna masa cewa babu bukatar ajiye kudin garkuwar kariyar asara, saboda kasuwancinmu na saye da sayarwa ne. A hakikanin gaskiya ya saurari daukacin korafinmu, sannan ya yi alkawarin yin aiki tare da mu, mu ma mun yi alkawarin hada karfi da shi don yi aiki tare, sannan za mu rika bayar da shawarwari a duk sa’adda bukata ta taso.
Aminiya: Ko ya amince da shawarwarinku ?
Gwadabe: E, ya amince da wasu daga cikinsu. daya daga ciki kuwa ita ce maganar miliyan 35 da za mu a ajiye a wani asusu da babu wata fa’ida ko karuwa a cikinsa. Sai muka sanar da shi cewa, a tsarin hada-hadar kasuwanci bai kamata a yi haka ba. Sai ya ce, e, zai yi nazari a kan haka. Sannan mun bukaci ya kara mana wa’adi. Wannan ma ya ce, e. zai duba. Sannan mun buaci a sake nazari kan karin kudin da aka kayyade mana na Naira miliyan 35, a matsayin sabon jari. A kan wadannan muka tsaya.
Aminiya: Ko kana da kwarin gwiwa a kan sabon Gwamnan Babban Banki?
Gwadabe: E, akwai tabbas, muna da tabbacin cewa sabon Gwamnan Babban Banki, Mista Godwin Emefiele, ba mu da wata hujjja ta yin tababa game da abin da ya fada, illa dai kawai muna cika aikinsa game da al’amuran (da muka bijiro masa da su).
Mun smau labarin cewa akwai ’ya’yan kungiyarku da ke gudanar da ayyukan da suka saba wa doka. Shin ba ka ganin ko sabon tsarin na da manufar rage yawan cibiyoyin hada-hadar canjin kudi a kasar nan?
Wannan haka yake. Mun fahimci cewa wannan babbar matsala ce. Don haka muka sanar da Gwamnan Babban Bankin cewa, maimakon ka rage yawan mutanen da ka fahimci suna aiwatar da haramtaccen ciniki, sai ka raba mu rukuni-rukuni, tunda a bankuna sai da aka kasa su kashi-kashi, wadanda suka hada da bankuna yanki da na duniya da kanana. Mun yi masa nuni da cewa kada ya dauka cewa muna adawa da cin gashin kai da aka bai wa bankuna. Muna ganin al’amarin da wata kima. Idan aka raba su gida-gida, wadanda za su iya kai gaci, za su kai, don yin hakan shi ne adalci, maimakon a yi mana kudin goro. Farfesa Soludo ya taba yin irin wannan tsari. Shi ya fito da shirin raba ’yan canji gida biyu, wato rukunin A ga masu canjin Dala, su kuwa rukunin B, wadanda ba za su iya cimma ajiye Dala dubu 200 ba. wadannan na daga cikin shawarwarin da muka bayar.
Aminiya: Ga shi dai a mako mai zuwa wannan wa’adi zai kare?
Gwadabe: E, muna sane, amma ba za mu iya cimma wa‘adin ba. Mun bayyana wa Gwamnan Baban Bankin. Ba za mu iya ba. Mun roke shi da ‘’yan Najeriya su fahimci cewa wa’adi ya yi mana kadan. Matukar ba a kara wa’adin ba , za a fahimci tunanin da muke yi na rashin yi mana adalci, sannan a ga cewa tsarin an fito da shi ne don a cutar da mu. A irin wannan yanayi da ake fama da matsalar tsaro, babu kudin hada-hada a tsarin da ake tafiya kai.
Mun kuma rubuta wasika ga fadar shugaban kasa, kamar yadda muka yi wa majalisr datijai. Muna rokonsu su, su duba wannan lamari.
A halin yanzu ba mu ga yiwuwar cim ma wannan manufa ba. Mun yi magana da ’ya’yan kungiyarmu, kowa sai korafi yake yi, cewa babu wanda zai iya cika sharuddan wannan wa’adin. Ina ganin kashi 10 cikin 100 na ’ya’yan kuniyarmu mutum dubu uku da 500 ba za su iya cim ma wa’adin ba. Ba na ganin yiwuwar hakan.
Yaya kake ganin yiwuwar hadewar  ’ya’yan kungiyarku?
Gwadabe: Tabbas, muna duba yiwuwar hakan. A hakikanin gaskiya wasu mutane sun fara tattaunawa kan al’amarin, amma abin da muke cewa ba zai yiwua a yi wata hadewa mai alfanu ba, cikin mako biyu. Lokacin da aka ba mu ba zai ba mu dama ba, ya zo mana ba cikin shiri ba . Wasu za su sayar da kadarorinsu ko su tafi bankuna don neman rance, ta yadda za su hada yawan kudin da aka kayyade, amma ai an san cewa lamarin ba zai yiwu ba, cikin mako biyu.
Aminiya: Akwai rikicin shugabanci a kungiyarku ta ABCON, shin ba ka ganin wannan na daga cikin kalubalen da kuke fuskanta?
E, na yarda da haka, amma matsalar da muke fuskanta ba yana nufin cewa daga wace kungiya mutum ya fito ba, sai dai yaya za a cim ma manufar  kasa. A hakikanin gaskiya, akwai kuniyoyi da suka fi kungiyarmu kudi, amma a ganina wannan ba matsala ba ce. Za mu gana da mutanenmu a daukacin shiyoyyi shida na kasar nan, cikin mako mai zuwa, don fitar da amtsaya ta bai daya kan wannan tsari, musamman kan al’amarin da ya shafin wa’adin da aka gindaya.
Za ka fahimci cewa, ba ma adawa da garambawul din da ake kokarin aiwatarwa a wannan fanni, don a gaskiya tsarin yana da kyau, kuma zai iya haifar mana da dimbin damar hada-hadar kasuwanci. A alkawarin da Gwamnan Babban Banki ya yi mana, ya bayyana cewa duk wanda ya cika ka’idojin da aka shimfida a sabon tsari, zai zama wakilin masu hada-hadar aikewa da kudi ta duniya, wato Western Moneygram.
Idan Gwamnan Babban Banki ya ki yin sassauci game da matakin da aka dauka, mene ne abin yi?
Abin takaicin shi ne cibiyoyin hada-hadar canjin kudi da dama za su daina hada-hada, ta yadda rashin aikin yi zai karu a kasa, kuma masu haramtaccen ciniki a kasuwannin bayan fage za su kara karfi, kuma kamfanoni da dama za su durkushe. Sannan bukatar da aka bijiro da ita ta ajiyar Naira miliyan 35 a a matsayin kudin kariyar asara ba shi da fa’ida, domin ba a ambaci yawan Dalar Amurka da Babban Bankin zai sayar ba, idan har aka cika ka’idar. A halin yanzu dai muna da kudin kariyar asara na Dala dubu 20, muna sayen Dala dubu 50 daga Babban Bankin Najeriya a kowane mako, ga shi ma yawan kudin ya ragu daga Dala dubu 50 zuwa 15 a kowane mako.