Sabon zababben Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Sagir Adamu Abbas ya karbi ragamar kama aiki a hukumance.
Farfesa Sagir, wanda ya gaji Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya karbi aikin ne a wani kwarya-kwaryar biki da ya gudana a farfajiyar sabon ginin hukumar makarantar a ranar Litinin.
A ranar Asabar, 8 ga watan Agusta ne dai Hukumar Gudanarwar Jami’ar ta tabbatar da nadin Sagir wanda Farfesa ne a fannin Lissafi a matsayin sabon shugaban makarantar.
Daga nan ne kuma sabon shugaban ya yi alkawarin tafiyar da mulkinsa ta hanyar yin komai a bude tare da jan kowa a jika don ganin hakar jami’ar ta cimma ruwa.
Ya yaba wa magabacinsa kan yadda ya kawo muhimman sauye-sauye a jami’ar, musamman ta bangaren gine-gine da habaka harkokin bincike, yana mai alkawarin dorawa daga inda ya tsaya.
“Farfesa Yahuza malamina ne; ya koyar da ni tun daga matakin digirin farko. Ya hidimta wa BUK daidai gwargwado kuma ina da kwarin gwiwar zai ci gaba da yin hakan”, inji Fasfesa Sagir.
Daga nan sai ya gode wa jami’ar kan zabar sa da ta yi a kan mukamin, tare da neman hadin kai da goyon baya domin ganin an kai jami’ar ga tudun mun tsira.