Sabon shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya Sanata Abdullahi Adamu, ya ajiye mukaminsa na Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Yamma a Majalisar Dattawan kasar.
Sanata Abubakar Kyari, dan majalisa mai wakiltar Borno ta Arewa, shi ma ya sanar da ajiye nasa mukamin.
Matakin ‘yan majalisun biyu ya biyo bayan zabarsu da aka yi kan sabbin mukaman da suka hada da shugabancin jam’iyyar APC mai mulkin na Najeriya na kasa, nauyin da a yanzu ya hau kan Abdullahi Adamu, yayin da shi kuma Abubakar Kyari ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar ta APC na yankin Arewacin Najeriya.
’Yan majalisar sun sanar da murabus din nasu ne cikin wasu wasiku daban-daban da suka aika zuwa zauren Majalisar Dattawan, wadanda shugaban majalisar Sanata Ahmad Lawan ya karanta a wannan Talatar.
A baya dai Sanata Adamu ne ke jagorancin Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin noma da raya karkara, yayin da Sanata Kyari ke shugabantar kwamitin kula da Abuja, babban birnin tarayya.