Wani sabon rikici mai kama da na kabilanci da ya barke a yankin kasuwar ’yan gwangwan da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun, ya yi sanadin raunata mutane da dama, cikinsu har da Sarkin Hausawan birnin, Alhaji Ibrahim Hassan Hassan.
Rahotanni sun ce wasu batagari ne suka kai masa hari suka sassare shi a lokacin da ya isa wajen domin yin sasanci.
- Kotu ta kori Gwamnan Ebonyi da mataimakinsa saboda komawa APC
- ‘Mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu sun haura miliyan 2’
Wani ganau a inda lamarin ya faru mai suna Hassan, ya shaida wa Aminiya cewa rikicin ya samo asali ne tun da safiyar Litinin, bayan wasu matasan da ya yi zargin na Yarbawa nesuka tare wani Bahaushe inda suka nemi su karbi kudi a hannunsa da karfi amma yaki yarda.
Hakan, inji Hassan, ya sa suka fasa masa kwalba a kansa, lamarin da ya janyo masa mummunan rauni, inda aka garzaya da shi asibiti har uku amma suka ki karbarsa kafin daga bisani wani asibitin suka karbe shi.
Sai dai ya ce daga bisani ya rasu da yamma.
“Mutuwarsa ce ta sanya wasu matasan Hausawa suka ce basu yadda ba, inda fada ya barke a tsakaninsu. ’Yan iska kuma suka fara fasa shagunan ’yan kasuwa suna sata, yanzu haka sun kone kusan rabin kasuwar ’yan gwangwan, an jikkata mutum bakwai yayin da mutum biyu suka rasa rayukansu.
“’Yan sanda sun zo domin su kwantar da tarzoma kuma yanzu halin da ake cike an rufe kasuwar, ba shiga, babu fita,” inji shi.
Kzalika, Muhammad, wani mazaunin Sabo Abeokuta ya shaida wa Aminiya cewa shi kansa Sarkin Hausawan Abeokuta said a aka sassare shi lokacin da ya je wajen da nufin yin sasanci.
“Sai da aka kai shi babban asibitin gwamnati na Abeokuta suka ki karbarsa kafin daga bisani aka kai shi Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya (FMC), inda ake kula da lafiyarsa a halin yanzu,” inji shi.
Mai taimaka wa Gwamnan Jihar ta Ogun, kan Harkokin Baki, Abdulhadi Sani, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin, inda ya ce, “Yanzu haka muna tare da Shugaban Karamar Hukumar Abeokuta ta Arewa muna ci gaba da karban wadanda aka raunata a rikicin, kuma zuwa yanzu kura ta fara lafawa bayan gwamnati da jami’an tsaro sun dauki kwararan matakai.”
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce tuni kura ta lafa bayan jami’ansu sun kwantar da tarzoma.
Sai dai ya ce ba zai iya fadin adadin wadanda suka jikkata ko suka rasa ransu a rikicin ba, har sai sun kammala binciken da suke yi a kai.