Sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Abubakar Lawal, ya kama aiki a Hedikwatar rundar jihar da ke Bompai.
An nada Lawal ne a ranar Laraba bayan tsohon Kwamishinan ’yan sandan jihar, Sama’ila Shuaibu Dikko, ya yi ritaya daga aiki.
- Yoyon fitsari: Za a yi wa mata 150 aiki kyauta da tallafi a Kano
- Abubuwa 10 da ke cikin Dakin Ka’aba
Dikko ya yi ritaya daga aikin dan sanda ne bayan ya cika shekara 60 da haihuwa a ranar 27 ga watan Yuli, 2022, kuma shi ne na 42 a jerin Kwamishinonin ’Yan Sanda da aka yi a jihar Kano.
Kafin yanzu Lawal, wanda shi ne Kwamishinan ’Yan Sandan JIhar na 42, ya kasance Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Inugu.