✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sabon kaura ta lashe kofin ‘FRESH’

A ranar Litinin ne kungiyar kwallon kafa ta Sabon kaura da ke garin Kafanchan ta lashe kofin shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Neja (NSFA)…

A ranar Litinin ne kungiyar kwallon kafa ta Sabon kaura da ke garin Kafanchan ta lashe kofin shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Neja (NSFA) kuma memba a kwamitin zartarwa a hukumar kwallon kafa ta kasa (NFF) Kwamred Yusuf Ahmed da ake yi wa lakabi da FRESH, karo na farko, bayan ta doke takwararta mai suna Shettima Rainbow Academy a bugun daga kai sai mai tsaron gida (fanariti).

Wasan, wanda aka gudanar da shi a sabon filin wasa na garin Kafanchan ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a harkar wasan kwallon kafa daga jihohi daban-daban.

Wasan, wanda aka shirya don sadar da zumunci da karfafa hadin kai a tsakanin jama’ar yankin, ya kunshi kungiyoyi goma sha biyu da suka fafata a gasar da suka hada da Young Boys (Aso) da Goska (Kaninkon) da Jama’a Emirate da SD Academy (Barde) da Police Academy (Atuku) da Araf (Kagoma) da 11 Warriors (Gidan Waya) sai Golden Barley (Kafanchan).

Sauran kungiyoyin sun hada da Takau FC da Sabon kaura da kuma Rainbow Academy.

Bayan an tashi canjaras ne aka yi bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ‘yan wasan Sabon kaura suka jefa kwallaye hudu suka zubar da daya su kuma ‘yan wasan Rainbow Academy suka zubar da kwallaye biyu ina aka tashi ci (4-3).

Kwamred Yusuf Ahmed (Sardaunan kwallon Najeriya) ya nuna farin cikinsa da shirya wannan wasa wanda yake nuni zuwa ga samun zaman lafiya da kuma fito da ‘yan wasa masu hazaka da kuma baiwar taka leda.

FRESH, ya nuna jin dadinsa ga wadanda suka dauki nauyin shirya gasar, tare da  yaba da yadda aka gudanar da wasan tun daga farawa har zuwa kammalawa ba tare da samun wata matsala ba inda a karshe ya yi fatan ci gaba da shirya irin wannan wasa.

A lokacin da yake jawabin godiya, shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kaduna Alhaji Shareef A.D kassim, ya nuna jin dadinsa tare da mika godiya ga manyan bakin da suka samu damar halarta daga jihohi daban-daban, inda ya sha alwashin ci gaba da shirya irin wadannan wasanni sannan ya yi fatan Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya.

Bayan kammala wasa an mika kyaututtuka ga dukkanin kungiyoyin da suka shiga gasar, tare da bayar da kofi da kuma kyautar naira dubu dari da dubu saba’in da dubu hamsin ga kungiyoyin da suka zo na daya da na biyu da kuma na uku bi da bi.

Daga cikin wadanda suka halarci wasan akwai Kwamishinan Matasa da Wasanni da kuma Al’adu na Jihar Kaduna, Honorabul Daniel A. danauta wanda shi ne ya wakilci gwamnan jihar.

Daga cikin mahalartan akwai shugabannin hukumar wasan kwallon kafa na jihohin Kaduna da Borno da Kano da Jigawa da Kogi da Nasarawa da Filato da shugabannin kungiyoyin kwallon kafa na Wikki Tourist da Plateau United da kuma tsohon dan wasan Najeriya dahiru Sadi.