✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kwato bindigogi da albarusai daga mutane

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama kanana da manyan bindigogi 178 da albarusai 840 da aka kwato daga hannun mutane a sassan jihar. Bindigogi…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama kanana da manyan bindigogi 178 da albarusai 840 da aka kwato daga hannun mutane a sassan jihar. Bindigogi 29  da albarusai 31 daga cikin makaman wadansu masu kishin kasa ne suka mika da hannuwansu ga rundunar a yayin da aka kwato bindigogi 149 daga hannun miyagun mutane.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Abiodun Odude ne ya fadi haka a lokacin da yake nuna wa ’yan jarida  makaman da aka baje kolinsu a harabar hedkwatar ’yan sandan da ke Eleyele a Ibadan.

Ya ce, nasarar kamen ta biyo bayan damuwar Sufeto-Janar Ibrahim Kpotun Idris ce a kan yawaitar makamai a hannun mutane a sassan kasar nan. Hakan ne ya sa Sufeto-Janar ya bayar da umarni ga Mataimakansa masu kula da shiyyoyi 12 su hanzarta daukar matakan kwato wadannan makamai daga hannun mutane.

Ya ce hakan ne ya sa Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta fara aiki da umarnin har ya kai ga kwato wadannan kanana da manyan bindigogi daga hannun mutane masu aikata miyagun ayyuka a jihar inji Kwamishinan. Ya ce, akwai wata karamar bindiga da Shugaban kasa kadai ne yake sanya hannun bayar da lasisin mallakarta da wani babban mutum da aka sakaya sunansa ya mika ta da hannunsa ga ’yan sanda domin aiki da umarnin mahukunta.

Mista Odude ya nemi mutanen da suka mallaki bindigogi su hanzarta mika su ga mahukunta domin bin doka da oda da kyautata tsaro a jihar da kasa baki daya. Ya ce, yanzu haka rundunar ta kara kama mutum 5 a kan mutum 16 da ta kama a makon jiya da ake zarginsu da aikata fashi da makami da garkuwa da mutane a yankin Igboho da Igbeti da Kishi.