✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronaldo ne zai lashe Gwarzon dan kwallon duniya na bana – Jaridun Sifen

A shekaranjiya Laraba ne wasu jaridun da ake wallafa su a kasar Sifen ciki har da jaridar Mundo Deportibo mai watsa labaran wasanni suka sanar…

A shekaranjiya Laraba ne wasu jaridun da ake wallafa su a kasar Sifen ciki har da jaridar Mundo Deportibo mai watsa labaran wasanni suka sanar da cewa shahararren dan kwallon kulob din Real Madrid na Sifen Cristiano Ronaldo ne zai lashe kyautar Gwardon dan kwallon duniya ta bana da aka fi sani da Ballon d’Or.

A binciken da jaridun suka gudanar, sun nuna Ronaldo shiga gaban Lionel Messi da Luis Suarez ’yan kwallon FC Barcelona da kuma Antoine Griezmann dan kwallon Atletico Madrid da suke fafatawa a gasar.
Jaridun sun nuna kawo yanzu kuri’un da Ronaldo ya samu sun dara na sauran abokan takazararsa da hakan ta nuna shi zai lashe kyautar.
Jaridun sun ce suna ganin dan kwallon zai samu nasarar lashe kyautar ce saboda nasarar da ya samu wajen taimakawa kulob Real Madrid lashe kofin Zakarun kulob na Turai (Champions League) a karo na 11 a bara da kuma yadda ya taimaka wa kasar haihuwarsa Fotugal wajen lashe kofin Nahiyar Turai (Euro) a karon farko a bara. Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya dan kwallon ya sha gaban wadanda suke fafatawa da shi, inji jaridun.
Wata jaridar da ke wallafa labaran kwallo a Faransa ce take daukar nauyin wannan gasa, kuma an nuna a ranar Litinin mai zuwa 12 ga watan Disamba ce za ta sanar da Ronaldo halin da ake ciki.
A ranar Litinin 9 ga watan Janairun 2017 ne za a sanar wa duniya Gwarzon dan kwallon duniya a bikin da Mujallar ta shirya tare da Hadin gwiwar Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma ta Nahiyar Turai (UEFA).
Idan Ronaldo ya lashe kyautar, zai kasance ya lashe sau hudu kenan a tarihin kwallonsa. Lionel Messi ne ya taba lashe kyautar har sau biyar.