✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ronadinho ya yi murabus daga taka leda

Tsohon dan wasan kasar Brazil da Barcelona, Gaucho Ronaldinho ya yi murabus daga tala leda. Wakilinsa mai suna Roberto Assis ne ya tabbatar da lamarin…

Tsohon dan wasan kasar Brazil da Barcelona, Gaucho Ronaldinho ya yi murabus daga tala leda.

Wakilinsa mai suna Roberto Assis ne ya tabbatar da lamarin ga manema labarai, inda ya ce, “Eh, Ronaldinho ya yi murabus. Mu fara shirin bikin yin murabus din shi, amma sai bayan gasar cin kofin duniya, watakila a watan Agusta. Za mu yi abubuwa da yawa a Brazil, Yankin Turai da Asiya, sannan kuma mu na da wani shiri da kungiyar kwallon Brazil.

Ronaldinho dai dan wasa ne mai matukar basira da ya kware wajen wasa da murza leda.

Ya fara wasa ne da kungiyar Gremio na kasar Brazil, daga nan ya kuma kungiyar PSG na Faransa a shekarar 2001.

Bayan gasar cin kofin duniya na shekarar 2002, inda Ronaldinho ya nuna iyawansa a fili, ciki hard a zura wa kasar Ingila kwallo day a yi daga tsakiyar fili da bugun tazara, ya sa akai ta rububu a kansa, daga karshe ya tafi kungiyar Barcelona a shekarar 2003.

A Barcelona ne tauraronsa ya matukar haskakawa inda ya har ya lashe gasar Laliga sau biyu da bugun gwanaye wato Champions League. Sannan daga bisani ya koma AC Milan a shekarar 2008, inda ya lashe gasar Serie A a shekarar 2010-2011.