✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Roko ga PDP

Edita alherin da Shema ke yi a Jihar Katsina, muke son ya watsu kowane lunguna kasr nan, kan haka muke rokon jam’ikyyar PDP ta Bamanga…

Edita alherin da Shema ke yi a Jihar Katsina, muke son ya watsu kowane lunguna kasr nan, kan haka muke rokon jam’ikyyar PDP ta Bamanga mai alamar lema da ta tsaida mana Shema 6ttakarar shugaban kasa a shekarar 2015. Magana ta gaskiya diyar sardauna irin su Shema kadai ke iya gyara Najeriya. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.
Rigimar PDP
Salam. Aminiya wannan rigima ta PDP Allah ka kara fadadatak tafi haka tsanani, muna fatan kada su shirya tsakaninsu, domin ‘’yuan najeriy su samu maslaha daga mummunan wahalar da kasa. Allah ya taimaki al’ummar najeriya, su fita daga matsalar PDP. Amin. Daga Adamu Suleiman Kaugama 0805767672400.

Sakonnin waya

Sara da sassaka

Kama ‘’ya’yan Sule Lamido da hukumar EFCC ta yi ba wani abu b ane illa bita dfa kullin siyasa, kuma wannan ya nuna cewa EFCC ta zama karyar farautar shugaban kasa. Kifi na ganinka mai jar koma. Gaba dai, gaba dai Sule Lamido. Daga Isah Sani Mai arsenal Garkon Alh. Jihar Jigawa 08072556844.

Ina tare da Aminiya
Salam Aminiya dubun gaisuwa da fatan alherin a ci gaba da fadar gaskiya komai dakinta. Allah na tare daku. Daga Zubair M. Fagge. 08034412272.

Ga Gwamnonin G7
Edita ka mika sakona ga Gwamnonin G7 da su hade da APC don ci gaban kasa, in dai don talaka suke yi. Daga Boska Gwarzo Jihar Kano 08108364482.

Kwankwaso da karan mahaukaciya
Gwamna Rabi’u Kwankwaso kana fama da karan mahaukaciya. Allah ya fidda A’i ga rogo lafiya. Daga Maryam A. Sanni 08086560647.

Aminiya ga amanar talakawa
Assalamu alaikum Allah Yasa Aminiya ta rike amanar mu talakawan Arewa. Domin ita ce abin da muke alfhari a Arewa. Daga Maraya Shanono Jihar Kano 08086560647.

Ga Gwamnan Gombe
Aminiya don Allah ku isar da kukana gun Gwamnan Gombe, Durbin Tangale. Mun ji aikin da kake yi don Allah ka manta da billerin Tayanna. Daga B.R. 08069585877.

Sanata Habu Ibrahim
Salam Amintattar jarida mai farin jini. Ina son ka isar min da sakon kirana ga Sanata Habu  Ibrahim da ya fito takarar Gwamnan Jihar Katsina, domin ya ceto mu daga bakin mulkin jam’iyyar PDP. Daga Nasiru kauyen dandago Musawa, Jihar Katsina 07068198138.

Hukumar NOA ga aiki a gabanki
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa NOA. Edita ku isar mani da sako a kan ta wayar da kan al’ummar kasa kan bambancin ayyukan shugaban kasa da na ’yan majalisar wakilai da dattijai na Tarayya da Gwamnoni da Shugabannin kananan hukumomi. Daga Haruna Sule Karkanna, Jihar Jigawa. 08034543843.

APC darama birnin Shehu
Mu kam Sakkwatawa muna nan da Bafarawa, domin shi ne jagoranmu, ya yi mana adalci ya taimaki matasa da aikin yi da ci gaban matasan Jihar Sakkawato. Me zai sa mu bar Bafarawa, muna nan sai garkuwa APC daram. Daga Musty Sak 08034068363.

Ga Sarkin arewan Bauchi
Assalamu alaikum. Don Allah Edita ka mika min martanina ga Alhaji Hassan a kan cewa wai Maulana Shehil Islam bai kyauta ba, a kan gaskiyar da ya faddi lallai ya cika mara adalci. Daga Uthman 07037159756.

Aminiya a isar min sakona ga ‘’yan majalisar dattawa, ina har ba su tsayawan ba akan maganar kudin da Madam Stella Oduah ta kwasa da kuma kudin bayin Allah na SURE-P da ‘’yan tsirarun mutane suka handame.  Daga A. S. Katsina. 08030981219

Ga masu shirin taron kasa
Aminiya ki isar min da sakon gaisuwa da nuna kwarin gwiwa ga irun su Adamu danjuma Isah bakin WAPA kan yadda suke kokari a wajen shirya taron makomar kasa tare da hadin gwiwar Kungiyarsu ta GAUTA CLUB. Daga Kabiru Fagge 08137373725.

Fatan alheri ga Aminiya
Assalamu alaikum Aminiya sunanan Yusuf Haruna Ummar  ina zaune, ina yi wa Aminiya fatan alheri. Ni mazaunin Zariya ne. Daga 08139618011.

Ga Gwamnatin Zamfara
Ina kira ga Gwamnatin Jihar Zamfara da ta yi wa Allah ta dauki mataki kan rashin tsarion da ya addabi garin dansadau da dangulbi da ke cikin karamar Hukumar Mulki ta Maru. A tausaya wa halin da al’umma ke ciki. Daga Nasiru Bello Gusau. 07068223562.