✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ritaya Sa!

Wani lokaci ne rundunar ’yan sanda ta zabi mutane ta horar da su, suka zama ’yan sanda. Bayan atisayen mako biyu sai aka zo tura…

Wani lokaci ne rundunar ’yan sanda ta zabi mutane ta horar da su, suka zama ’yan sanda. Bayan atisayen mako biyu sai aka zo tura mutane garuruwan da za su fara aiki. Aka rika kiran mutane da garuruwan da aka tura su, wasu Legas, wasu Zamfara da Katsina da Jigawa. Kowa aka kira sunansa da garin da aka tura shi, sai ya ce yes Sa! Ana cikin haka sai mai kiran sunan ya ce: “Ibrahim Jankada, Maiduguri”
Sai Ibrahim ya zabura, ya ce: “Ritaya, Sa!”
Daga Bashir Musa Liman 07036925654