Yayin da Shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan da wasu Gwamnonin jihohi suke ta shirye-shiryen mika mulki ga wadanda za su gaje su, wata rigima na can ta kaure tsakanin bangaren Zartaswa da na Dokoki a jihohin Kebbi da Neja da Enugu. Jihohin Enugu da Neja, jam`iyyar PDP ke mulki, tun da aka dawo mulkin dimukradiyya yau shekaru 16, yayin da a jihar Kebbi kuwa ANPP ta fara yin mulki na shekaru 8, 1999 zuwa 2007, a zaman jam`iyyar adawa ga jam`iyyar PDP. Jam`iyyar PDP, ita ta karba a shekarar 2007 zuwa yau wato 2015. Yanzu maganar da ake jihar Enugu ce kadai jam`iyyar PDP za ta ci gaba da mulkinta a wannan karon, yayin da a jihohin Neja da Kebbi, jam`iyyar APC ce za ta karbi ragamar mulkinsu daga ranar 29 ga wannan watan na Mayu. A dukkan wadannan jihohi uku `yan Majalisar Dokokin jihohin ne ke barazanar sai sun tsige Gwamnoninsu kafin nan da cikar wa`adin saukarsu 29 ga wannan watan.
Alal misali a jihar Kebbi inda a ranar 29 ga watan Afrilun da ya gabata kwana daya tak, bayan Majalisar Dokokin jihar ta tsige Kakakinta Alhaji Hassan Mohammed Shalla da mataimakinsa, ta kuma mayar da tsohon shugabanta Alhaji Musa Jega, da ta tsige a a cikin watan Nuwamban bara, Majalisar Dokokin jihar ta aika wa da Gwamnan jihar Alhaji Sa`idu Usman dakingari da wata takarda dauke da laifuffuka guda shidda da suka ce sun cancanci ta tsige shi. Laifuffukan sun hada da ciwo bashin Naira biliyan biyu, daga asusun bankunan inganta tattalin arziki ga masu kananan harkokin kasuwanci, ba tare da tuntubar Majalisar Dokokin jihar ba. Akwai kuma zargin ya hamdame kusan naira biliyan biyu, da sunan zabubbukan bana, ba ya ga wasu N965miliyan da sunan ayarin jihar ya kai ziyara ga shugaban kasa da mataimakinsa da uwargidan shugaban kasar a Abuja da dai sauransu zarge-zarge.
Tuni dai Gwamnan jihar na Kebbi ya musanta wadancan zarge-zarge, ya kuma dage a kan cewa, gwamnatinsa ba za ta yi aiki da sabon Kakakin Majalisar Dokokin jihar ba, shi tsohon ya saniAlhaji Hassan Shalla. An shiga zaman doya da manja a jihar ta Kebbi tsakanin Majalisar Zartaswar jihar da ta Dokoki da wasu jiga-jigan jam`iyyar PDP na jihar, tun a bara bayan da Gwamna dakingari ya yi gaban kansa ya nada Manjo Janar Bello Sarkin Yaki a zaman dan takarar neman mukamin Gwamnan jihar a inuwar jam`iyyar ta PDP da wasu `yan takarar.Wannan ya sanya wasu `yan Majalisar Dokokin jihar 12 da wasu jiga-jigan jam`iyyar suka canja sheka daga jam`iyyarsu ta PDP zuwa jam`iyyar adawa ta APC, a lokacin, bare kuma yanzu sakamakon zaden banan ya tabbatar wa da jam`iyyar ta APC gagarumar nasara a jihar ta Kebbi.
A can jihar Neja, irin wannan hali na barazanar tsige Gwamnan jihar Alhaji Mu`azu Babangida Aliyu yake fuskanta daga wasu`yan Majalisar Dokokin jihar, bayan zaman dasawar kusan shekaru takwas da suka yi. A ranar Talatar makon jiya kwatsam Majalisar Dokokin jihar ta Neja ta tsige Kakakinsu Barista Adamu Usman, ta maye gurbinsa da Alhaji Isa Kawu. Kashegari kuma `yan Majalisar suka nemi su zauna da aniyar su tsige Gwamnan jihar, amma `yan sanda suka hana su shiga zauren Majalisar ta hanyar jefa masu hayaki mai sa hawaye da ya tarwatsa su. Ana cikin wannan dambarwa Gwamnan jihar ya samu zaunawa da `yan Majalisar Dokokin, inda wai suka jaddada masa goyon bayansa, na ci gaba da yin aiki tare, kamar yadda Kakakin Gwamnan Mista Isra’el Ebije, ya fada wa manema labarai a Minna babban birnin jihar. Duk da wannan amma kuma Gwamnan ya zagaye, ya je ya shigar da kara a babban Kotun jihar, wadda daga bisani ta bayar da hukuncin wucin gadi,na dakatar da `yan Majalisar a kan kada su kuskura su buda batun tsige Gwamnan har sai ta saurari shari`ar ta kuma yanke hukunci,ta kuma tsaida ranar 27 ga wannan watan ta zama ranar da za ta fara sauraren karar.
Babban abin da aka ce ya hada Gwamnan da Majalisar Dokokin jihar shi ne, zargin rike mata kudadenta na gudanar da ayyukan yau da kullum da suka kai naira biliyan daya, al`amarin da `yan Majalisar suka ce ya haddasa tsayawar ayyukansu cik. A jihar ta Neja ma akwai adawar Mataimakin Gwamnan jihar da wasu `yan Majalisar Dokokin jihar da wasu makarraban jam`iyyar ta PDP, sun canja sheka zuwa APC da kuma dadin dadawa irin kayin da jam`iyyar ta PDP ta sha a hannun APC, a zabubbukan da suka gabata.
A jihar Enugu, ma `yan Majalisar Dokokin jihar su 15, daga cikin 24, suka sa zaren lalle sai sun dambace Gwamnan jihar Cif Sulliban Chime kafin nan da barinsa karagar mulki a ranar 29 ga wannan watan. Zarge-zargen da `yan Majalisar suke wa Gwamnan nasu sun hada da yin jabun kwarya-kwaryar kasafin kudin jihar na naira biliyan goma sha biyu da kuma karin kudaden kwangilar gina sabuwar Sakatariyar jihar daga naira biliyan sha uku zuwa naira biliyan ashirin da daya, da kuma bayar da kwangilar ga kamfanin kwangila na Arab Construction, maimakon wani Kamfani da ya gabatar zai iya aikin a kan kudaden da ba su kai na Kamfanin na Arab din ba.
Saboda damuwa da rigimar kar ta yi tasiri a cikin sabon mulkinsa, tuni zababben Gwamnan jihar Cif Ifeanyichukwu Lawrence Ugwuanyi, ya shiga cikin maganar, inda ya gana da bangarorin biyu. Ganawar da ya zuwa yanzu ta haifar da `yan Majalisar suka mayar da wukakensu cikin kubensu, har suka kai ga sanar da jami`an tsaron jihar cewa sun rufe Majalisar Dokokin jihar har sai illa-masha Allah, ko kuma idan bukatar hakan ta gaggawa ta taso.
Mai karatu idan ka tattara wadannan barazana gaba daya za ka iya fahimtar cewa babban abin da ya kara rura wutarta bai wuce irin yadda dukkan wadannan Gwamnonin jihohi uku suka kammala wa`adinsu na biyu, dadin-dadawa kuma biyu daga cikinsu (Neja da Kebbi), jam`iyyarsu ta PDP warwas, a zabubbukan da suka gabatan, don haka `yan Majalisun nasu suke ganin ba su da wani tasirin a je a karasa tafiyar siyasar jiharta gaba. Akwai kuma zargin cewa `yan Majalisun Dokokin suna cikin tararrabin ta ina makudan kudaden sallamarsu za su fito daga irin yadda su kansu Gwamnonin suka koka a kan jihohinsu ba su da koda kudaden da za su biya albashin ma`aikatan jihohinsu. Dadin-dadawa wasu na ganin tunda Gwamnonin ba za su iya biyansu kudaden sallamarsu a kan kari ba, to, gara su tsige su (Gwamnonin), ta yadda su ma za su sauka ba tare da sun samu garabasar da za a biya takwarorinsu ba. Rikicin dai bai wuce son kai ba amma ba wai don talakawa ba.