✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sudan: Fada ya barke bayan sanarwar tsagaita wuta

An ci gaba da luguden wuta a birnin Khartoum sa'o'i kadan bayan sojoji da 'yan tawayen kasar sun amince su tsagaita wuta domin bikin Karamar…

An ci gaba da luguden wuta a Khartoum, fadar kasar Sudan, sa’o’i kadan bayan sojojin kasar sun amince da tsagaita wuta na kwana uku tsakaninsu da ’yan tawaye.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa jiragen yaki sun kai hare-hare a ranar Juma’a da ake bikin Karamar Sallah, ranar da sojojin suka amince da tsagaita wuta.

Aminiya ta ruwaito cewa, sojoji da ’yan tawayen da ke yakar juna sun amince su tsagaita wuta na kwana uku domin ba wa ’yan kasar damar yin bukukuwan Karamar Sallah.

Rundunar sojin Sudan ce ta sanar da amincewarsu da tsagaita wuta a tsakaninsu da ’yan tawaye daga ranar Juma’a, wadda ta kasance ranar Karamar Sallah a kasar.

Sanarwar da sojojin suka fitar ta ce, “Sojoji za su mutunta duk sharuddan yarjejeniyar tsagaita wutan da kuma dakatar da duk wani matakin soji da ke iya kawo tasgaro”

Sun sanar da haka ne bayan a safiar ranar ’yan tawayen RSF da suka shafe mako guda suna gwabza yaki da sojojin sun amince su tsagaita wuta na tsawon kwana uku.