✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin shugabanci ya lakume rayuka 56 a Sudan

An ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun Sudan da runduna ta musamman har zuwa safiyar Lahadi.

An ci gaba da gwabza fada tsakanin dakarun sojin Sudan da runduna ta musamman har zuwa sanyin safiyar Lahadi a babban birnin kasar Khartoum, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 56 tare da jikkata 170.

A ranar Asabar ce wannan rikici ya kaure, inda aka yi ta jin kararrakin harbe harbe da fashe fashe daga babban birnin kasar.

Daga bisani a ranar Asabar din runduna ta musamman ta yi ikirarin karbe iko da filin tashi da saukar jiragen sama na birnin Khartoum da sauran muhimman wurare.

Sai dai rundunar sojin Sudan ta musanta ikirarin, inda a wata sanarwa da ta fitar a daren Asabar take kira ga al’ummar da ke yankunan da abin ya shafa su kasance a cikin gidajensu a yayin da take ci gaba da luguden wuta a sansanonin dakarun na musamman din wato RSF.

Rikicin ya barke ne bayan da aka shafe makonni ana zaman tankiya tsakanin jagoran gwamnatin sojin kasar, Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa, da kuma kwamandan runduna ta musamman na kasar, Hamdan Daglo.

Hamayya tsakinin sojojin da rundunar RSF wadda aka kirkiro tun a shekarar 2013, ya samo asali ne tun lokacin mulkin shugaba Omar al-bashir, wanda aka hambarar a shekarar 2019.

Karkashin al-Bashir, dakarun ‘yan sa kai da Janar Mohammed Hamdan ke jagoranta, ta samo asali ne daga tsoffin tsagerun da aka fi sani da Janjaweed, wadanda suka kai mummunar farmaki a yakin Darfur na kasar Sudan a tsawon shekaru da dama aka kwashe ana rikici a can.

Bayanai sun ce, al-Bashir ya yi amfani da kungiyar wajen muzguna wa ’yan tsirarun kabilu wadanda ba Larabawa ba a Yammacin Darfur, lamarin da yanzu ya janyo masa tuhumar aikata laifukan yaki.

Tun a ranar Alhamis rundunar sojin Sudan ta yi gargadi kan yiwuwar barkewar arangama da dakarun sa kai na kasar masu karfi, wadanda ta ce an girke su a babban birnin kasar da sauran wasu yankun ba tare da amincewar sojoji ba.

A ’yan watannin baya bayan nan dai ana takun saka tsakanin sojoji da ’yan sa kai na farar hula, da aka fi sani da Rapid Support Forces ko RSF, lamarin da ya tilasta jinkirta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kasashen duniya ke mara wa baya da jam’iyyun siyasa domin komar da kasar kan mulkin dimokuradiyya.

A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar sojin ta ce jibge dakarun RSF a birnin Khartoum da sauran wurare a kasar an yi shi ne ba tare da amincewa ba, ko kuma hada kai da jagorancin sojoji kuma wannan karara an karya doka.

A baya bayan nan ne rundunar ’yan sa kai ta tura dakarunta zuwa kusa da garin Merowe na Arewacin Sudan.

Har ila yau, faifan bidiyo da ya rika yawo a kafafen sada zumunta tun a ranar Alhamis din, sun nuna wasu motoci dauke da makamai na RSF da ake jigilar su zuwa birnin Khartoum, zuwa Kudancin kasar.

Tashin hankalin na baya bayan nan tsakanin sojoji da jami’an tsaro ‘yan sa kai ya samo asali ne daga rashin jituwa kan yadda ya kamata a shigar da RSF a cikin sojoji da kuma yadda hukuma ya kamata ta kula da aiki.

Hadakar dai wani muhimmin sharadi ne na yarjejeniyar mika mulki Sudan da ba a saka hannu ba.

AP