Al’ummar Musulmi sun bukaci Gwamna Seyi Makinde ya kawo karshen rikicin da ke tsakanin Soun na Ogbomoso, Mai Martaba Oba Afolabi Ghandi Olaoye da Babban Limamin garin Sheikh Teliat Yunus Ayilara, kafin abin ya kazance.
Gamayyar Kungiyoyin Musulmi a Jihar Oyo (MUSCOYS) sun kuma yi kira gare shi, a matsayinsa na shugaban tsaron jihar ya hanzarta daukar matakin kawo karshen muhimman abubuwa biyu da suka shafi rayuwar Musulmi a jihar.
Na farko da suke neman a magance shi gaba daya kafin ya kazance shi ne jayayyar da ta ki ci ta ki cinyewa tsakanin Mai Martaba Soun na Ogbomoso da Sheikh Teliat Yunus Ayilara.
Abu na biyu shi ne rikicin da ya taso bayan wani fasto ya dauko sojojin haya suka lakada wa wani malamin addinin Musulunci da iyalinsa duka suka raunata su saboda sun yanka dabbar Layya tana fuskantar ginin cocin faston.
Shugaban kungiyar, Alhaji Ishaq Kunle Sanni da Sakatare, Alhaji Murisiku Abidemi Siyanbade, sun bayyana cewa kungiyar tana sane da cewa akwai kararrakin da aka shigar a kan wannan batu a kotu, amma duk da haka, Gwamna Seyi Makinde a matsayinsa na shugaban tsaro a jihar Oyo yana da damar daukar matakin yin gyara da magance wadannan al’amura domin kare lafiyar al’umma da dukiyarsu.
Sanarwar ’yan jarida da suka fitar a Ibadan a ranar Talata ta ce kungiyar ta (MUSCOYS) ta nuna bacin ranta a kan wasikar gargadi da Soun na Ogbomoso ya aika wa Babban Limamin a lokacin da yake kan hanyar tafiya kasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana.
Kungiyar ta bayyana cewa kafin ta kai ga daukar wannan mataki na yin kira ga Gwamna, sai da Kwamitin Dattawan Musulmi a jihar a karkashin jagorancin Farfesa D.O.S. Noibi da Sarkin Musulmin Yarbawa, Alhaji Dawud Makanjuola Akinola, suka jagoranci tawagar dattawan Musulmi da masu fada a ji zuwa garin Ogbomoso a inda suka samu ganawa da bangaren Sarkin da na limamin garin ba tare samun nasara ba.
Saboda haka take ganin Gwamna Seyi Makinde ne kadai zai iya yi maganin wannan lamari kafin abin ya kai ga kazancewa.