An yi ba ta kashi tsakanin jami’an ’yan sanda da ’yan kasuwar Sabon Gari da ke jibar Kano.
Rikicin ya barke ne a daidai lokacin da ’yan kasuwar ke gudanar da zanga-zangar kin mincewa da matakin Gwamnatin Jihar Kano na hana gudanar da kasuwanci a gefen titin kasuwar.
‘Yan kasuwar wadanda suka faro zanga-zangar daga titin France Road har zuwa bata sun kona tayoyi a kan titunan kasuwar.
A bangare guda kuma jami’an ‘yan sanda sun mayar da martani a kan masu zanga-zangar, inda suka rika fesa musu hayaki mai sa hawaye.
Masu zanga-zanga sun jikkata ‘yan sanda
Aminiya ta ruwaito cewa yayin gudanar da zanga-zangar an yi wa wasu jami’an yan sanda rotsi a daidai lokacin da suke kokarin tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun kiyaye doka da oda kamar yadda wani ganau mai suna Talle Dantata ya shaida wa wakiliyarmu.
Wani daga cikin masu zanga-zanga mai suna Musa Yahaya ya bayyana cewa sun gudanar da zanga-zangar ne saboda rushe musu wuraren neman abincinsu da gwamnatin ta yi.
‘Yaya za mu yi da rayuwarmu?’
“Yau kwanaku uku ke nan gwamnatin yi mana wannan cin mutumcin. Kuma wannan rusau da aka yi mana ba a yi mana adalci ba domin ba a ba mu wadataccen wa’adi ba. Kwana uku kawai aka ba mu.
“Yaya ake so mu yi da rayuwarmu? Ba mu gama farfadowa daga halin da muka shiga sakakon anmobar cutar corovirus ba, sannan kuma ga shi mun shiga wani”, iji shi.
Shi ma wani dan kasuwar wanda ya bayyana cewa ya kwashe sama da shekara 30 yana sayar da kayan marmari a wannan wuri ya bayyana cewa, “Ban san inda zan koma ba. Ga iyali da iyayena da ke karkashina. A yanzu haka kwananmu uku ba mu gudanar da kasuwanci a wannan wuri ba”.
Tun a ranar Juma’a dai Gwamnatin Jihar Kano ta fara rushe rumfunan tamfurare a gefen kasuwar ta Sabon Gari.
Gwamnai ta ba su wa’adin wata shida
Sai dai Gwamnatin Jihar Kano ta bakin Shugaban Hukumar da ke Kula da Hanyoyi ta Kihar wato KAROTA, Baffa Babba Danagundi ta musanta zargin na ‘yan kasuwar a kan rashin ba su wadataccen waadi.
Ya ce gwamnatin ta ba ‘yan kasuwar wa’adin watanni shida cewa su tashi, kasancewar suna zaune a wurin ne ba bisa ka’ida ba.
Duk kokarin Aminiya don jin ta bakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano a kan faruwar lamarin ya ci tura.
Kakakin Rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa bai amsa kiran waya da sakon kar-ta-kwana da aka yi masa ba.
Karin bayani na tafe…