Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), a ranar Alhamis ya bayyana cewa allurar rigakafin cutar Coronavirus miliyan 16, za ta iso Najeriya nan da wani lokaci.
Wakilin asusun a Najeriya, Mista Peter Hawkins ne ya sanar da hakan a garin Akure, yayin da ya kai ziyara ga Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu.
- Dole ce ta sa makiyaya suka fara amfani da AK-47 – Gwamnan Bauchi
- Ya kamata a hana makiyayan kasashen waje shigowa Najeriya kiwo – Ganduje
- Har yanzu El-Rufai bai fahimci batun matsalar rashin tsaro ba — Ganduje
- Yadda ’yan bindiga suka kashe mijina wata daya da aurenmu
Ya ce, “Yanzu muna kokarin ganin yadda za a kawo wa Najeriya allurar rigakafin COVID-19, wadda za a yi wa kaso 40 na al’ummar Najeriya.
“Yanzu muka yi rabi, za mu ci gaba da kokari don cutar zata iya kai wa nan da shekara daya ko biyu bata wuce ba.
“An yi yunkuri da dama don ganin Najeriya ta samu rigakafin, tare da rabata ta hanyar da ya dace,” inji shi
A nasa jawabin, Gwamna Akeredolu na jihar Ondo, ya jinjinawa UNICEf kan yadda take taimakon karatun ‘ya’yan jihar tsawon shekaru masu yawa.